Matatar Dangote Ta Shigar da Gwamnatin Bola Tinubu Kotu
- Matatar Dangote ta sake shigar gwamnatin Najeriya kara a yunkurin naman soke lasisin shigo da mai da aka bai wa ‘yan kasuwa da kamfanin NNPCL
- Rahoto ya nuna cewa hukumar kula da harkokin mai ta kasa ta NMDPRA kwanan nan ta bai wa ‘yan kasuwa shida lasisin shigo da man fetur
- Takardun kotu da manema labarai suka gani sun nuna cewa karar na neman soke lasisin shigo da mai da aka bai wa NNPC da wasu ‘yan kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matatar Dangote ta shigar da babban lauyan gwamnatin Najeriya kara domin neman soke lasisin shigo da mai da aka bai wa ‘yan kasuwa da kamfanin man fetur na gwamnati (NNPCL).
Shari’ar na nuna sake barkewar takun saka kusan shekara guda bayan Dangote ya janye wani kara da ya taba shigarwa kan irin wadannan lasisi.

Kara karanta wannan
An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe

Source: Getty Images
Dangote ya shigar da gwamnati kotu
Reuters ta wallafa cewa karar da Dangote ya shigar a yanzu na neman soke lasisin shigo da mai da aka bai wa Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) da wasu ‘yan kasuwa.
Sabuwar karar na neman Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta soke lasisin shigo da mai da Hukumar NMDPRA ta bayar ko ta sabunta, tana mai cewa hakan ya karya wani umarnin baya da aka bayar na ci gaba da tsayawa kan yadda al’amura suke.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar NMDPRA ba ta yi martani nan take ba kan bukatar yin tsokaci game da lamarin, sai dai ana jiran bayani daga gare ta.
Martanin 'yan kasuwa ga Dangote
Punch ta wallafa cewa a baya wasu masu kula da harkar da ‘yan kasuwa sun kafa hujjar cewa ana bukatar shigo da mai domin tabbatar da wadataccen mai tare da hana karancinsa.
A cikin karar, Dangote ya ce lasisin da aka bayar a wannan watan zai kawo cikas ga ayyukansa kuma sun saba wa doka, wadda a cewarsa ta amince da shigo da mai ne kawai idan samar da mai a cikin gida bai wadatar ba.
Dangote ya kawo karshen karar da ya taba shigarwa a watan Yuli na 2025 ba tare da bayyana dalili ba, lamarin da ya bar tambayoyi kan gasa da samar da mai a daya daga cikin manyan kasuwannin mai na Afirka.

Source: Getty Images
Batun shigo da mai daga waje
Najeriya ta dade tana dogaro da shigo da fetur daga waje saboda matatun man gwamnati da ba sa aiki yadda ya kamata.
An bayyana matatar Dangote mai darajar dala biliyan 20, mai karfin tace ganga 650,000 a rana, a matsayin hanyar kawo karshen wannan lamari, amma har yanzu ana ci gaba da shigo da mai daga ketare.
Kalubalen da Dangote ya fuskanta
A wani labarin, mun kawo muku cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta wajen gina matatar mai a jihar Legas.
A wata hira da aka yi da shi, Dangote ya ce ya yi fama da al'ummar da suke son hana shi gina matatar tun daga wajen mallakar filin gina ta.
Bugu da kari, ya ce masu shigo da man fetur daga ketare da masu cin gajiyar kudin tallafin mai ne gaba-gaba wajen ganin bai yi nasara ba.
Asali: Legit.ng
