Tana Ƙasar Waje: Lauyan Sadiya Farouk Ya Fadi Abin da Ya Hana Ta Zuwa Ofishin Kotu
- Tsohuwar minista a zamanin Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ta ce tana ƙasar Masar domin jinya a yayin da kotu ta bayar da umarnin ta gurfana a gabanta
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na tuhumar tsohuwar Ministar da wasu mutum biyu kan zargin karkatar da kuɗi da cin amanar aiki
- Kotun da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da sammacin kama Hajiya Sadiya Farouq, tare da dage shari'ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Tsohuwar ministar harkokin jin-ƙai da walwalar jama’a ta tarayya, Sadiya Umar Farouq, tana ƙasar Masar domin jinya kuma ba ta cikin ƙoshin lafiyar da za ta iya bayyana a gaban kotu, kamar yadda lauyanta ya sanar.

Kara karanta wannan
Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya
Lauyan nata, Mista Oladipo Okpesheyi, ya bayyana hakan ne yayin zaman kotun babban birnin tarayya da ke Apo a MM CF Sranar Litinin.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sadiya Umar Farouq tare da Bashir Nura Alkali, babban sakatare a ma’aikatar, da wani Sani Mohammed na fuskantar tuhume-tuhume guda 21 da hukumar EFCC ta shigar a kansu.
Tuhumar da EFCC ke yi wa Sadiya Farouk
Jaridar Daily Nigerian ta kawo labarin cewa hukumar EFCC ta zarge su da laifuffukan cin amanar aiki da kuma karkatar da wasu kuɗaɗen gwamnati.
Ana zargin tsohuwar ministar da waɗanda ake ƙara tare da ita da karkatar da kusan Dala miliyan 1.3 da kuma Naira miliyan 746.6.
Tun a watan Afrilu, 2026 ne kotun ta bayar da sammacin kama Sadiya Umar Farouq da Bashir Nura Alkali, yayin da EFCC daga baya ta ayyana tsohuwar ministar a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo.
A zaman kotun na ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026, lauyan EFCC, Rotimi Jacobs SAN, ya bayyana wa kotu cewa an shirya zaman ne domin gurfanar da waɗanda ake tuhuma.
EFCC ta magantu kan rashin bayyanar Sadiya
Sai dai lauyan EFCC, Rotimi Jacobs SAN ya nuna damuwa kan rashin halartar Sadiya Umar Farouq kotu ba tare da wani dalili ba.
Jacobs ya tunatar da kotu cewa tun a ranar 16 ga Afrilu, 2026 aka bayar da sammacin kama wadda ake ƙara ta farko.

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa bayan umarnin kotun ne Bashir Nura Alkali ya miƙa kansa ga EFCC domin biyayya ga umarnin da aka bayar.
Da yake jawabi, lauyan Sadiya Umar Farouq ya ce an sanar da shi cewa tsohuwar ministar na fama da rashin lafiya a ƙasar Masar.
A cewarsa, likitocin da ke kula da ita sun tabbatar da cewa ba ta da ƙarfin halartar zaman kotu a yanzu kamar yadda aka bukata.
Lauyan ya ce: “Muna roƙon kotu da ta ba mu lokaci saboda tana buƙatar kusan wata biyu kafin ta murmure."
Hukumar EFCC na neman tsohuwar Minista
A baya mun wallafa hukumar EFCC ta ayyana neman tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dukiyar talakawan Najeriya.
A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta EFCC ta ce wuri na karshe da aka ga Sadiya shi ne a Abuja, inda ta roki 'yan Najeriya su kai rahoto idan sun ganta a cikin gaggawa domin fuskantar tuhuma.
A ranar 16 ga Afrilu, 2026, babbar kotun tarayya da ke Apo, Abuja ta bayar da sammacin kama Sadiya Farouk bayan ta ki halartar zaman kotun da aka fara shari'a da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

