Dangote Ya Fadi Yadda aka So Durkusar da Matatar Shi tun wajen Sayen Fili

Dangote Ya Fadi Yadda aka So Durkusar da Matatar Shi tun wajen Sayen Fili

  • Aliko Dangote ya ce wasu ƙungiyoyi masu ƙarfi da ke cin gajiyar tsarin tallafin man fetur da shigo da mai a Najeriya sun yi ƙoƙarin dakatar da gina matatar sa ta Dala biliyan 20
  • Ya bayyana cewa ‘yan kasuwa, masu jigilar kaya, da sauran waɗanda ke amfana da tsarin tallafin sun tsorata cewa za su rasa biliyoyin Naira idan matatar ta yi nasara
  • Dangote ya ce matatar a yanzu tana rage dogaron Najeriya kan shigo da mai daga waje, kuma ana sa ran za ta ƙara adadin an da ta ke tacewa zuwa ganga miliyan 1.4

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana irin gagarumar adawa da ya fuskanta yayin gina matatar sa ta Dala biliyan 20 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba da mamaki, ya ki tsayawa takarar sanata a 2027

A cewar Dangote, wasu manyan mutane da ke amfana da tsarin shigo da mai da tallafi a ƙasar sun yi ƙoƙarin hana aikin yin nasara.

Alhaji Aliko Dangote
Aliko Dangote a hagu da matatar shi a gefen dama. Hoto: Dangote Industries|Getty Images
Source: Facebook

Da yake magana a wata hira da Nicolai Tangen, Dangote ya bayyana cewa masu adawa da shi sun hada da ‘yan kasuwa, masu jigilar kaya da wasu da ke samun riba mai yawa daga tallafin mai da shigo da man fetur.

Kalubalen da Dangote ya fuskanta

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa masu cin gajiyar tallafin mai sun ji tsoron matatar za ta rusa tsarin da ke samar musu biliyoyin Naira.

Punch ta rahoto ya ce sun yi amfani da hanyoyi daban-daban domin jinkirta aikin, ciki har da wahalar da aka sha wajen samun fili da za a gina matatar.

A cewarsa, samun fili ya ɗauki kusan shekaru biyar. Wani wurin da aka zaɓa ya tsaya cak tsawon shekaru uku da rabi, yayin da wani kuma ya fuskanci jinkiri fiye da shekara guda saboda ƙoƙarin hana ci gaban aikin.

“Duk wannan da a ce sun yi nasara, da sun hana mu ci gaba da magance waɗannan matsaloli,”

Kara karanta wannan

Uwargida ta cinna wa kishiyarta da ƴaƴanta 2 wuta a Kano, bayanai sun fito

In ji shi.

Duk da cikas ɗin, Aliko Dangote ya ce ya ci gaba da ƙudurin kammala aikin matatar, wanda ya kammala aikinta a lokacin marigayi Muhammadu Buhari.

Aliko Dangote da ma'aikatan shi
Lokacin da matatar Dangote ta fara tace man fetur. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Biliyoyin tallafin man fetur

Dangote ya kuma soki dogaro da Najeriya ke yi kan shigo da kayayyakin mai duk da kasancewar ƙasar ɗaya daga cikin manyan masu fitar da ɗanyen mai a Afirka.

A korafin da ya yi, Aliko Dangote ya ce shirin tallafin mai kaɗai yana cin kusan Dala biliyan 10 a kowace shekara a Najeriya.

Ya bayyana cewa wasu ƙungiyoyi — ciki har da ‘yan kasuwar mai, kamfanonin jigilar kaya, da masu rabon kaya — suna samun riba mai yawa daga tsarin, don haka suna adawa da duk wani sauyi da zai iya cutar da su.

“Wadannan su ne mutanen da ba sa son mu samu nutsuwa saboda suna ganin za mu zo mu kore su daga kasuwanci. Kuma hakika, wannan shi ne abin da muka yi yanzu,”

Kara karanta wannan

Ikuku: Rahama Sadau ta yi ta'aziyyar rasuwar jarumin fim a Najeriya

In ji shi.

TUC ta nemi a hada kai da Dangote

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar kwadago ta TUC ta bukaci gwamnatin Najeriya ta shiga hadaka da matatar Dangote.

TUC ta ce ko da gwamnati ba za ta dawo da tallafin mai ba, ya kamata ta hada kai da Aliko Dangote domin samar da shirin da zai rage kudin fetur.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke karuwa a Najeriya tun da Amurka/Isra'ila suka kaddamar da hare-hare a Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng