Sadiya Umar-Farouk Ta Burma Wata Matsalar, EFCC Ta Ba Ta Wa’adin Awanni 72

Sadiya Umar-Farouk Ta Burma Wata Matsalar, EFCC Ta Ba Ta Wa’adin Awanni 72

  • Babu makawa sai Sadiya Umar-Farouq ta amsa gayyatar da hukumar EFCC ta aika mata zuwa hedikwatarta a birnin Abuja
  • ‘Yar siyasar ta ki zuwa gaban jami’an da ke binciken abubuwan da su ka faru a ofishinta da sunan tana da rashin lafiya
  • EFCC ta sanar da lauyan Sadiya Umar-Farouk cewa sai ta taka kafa ta je wajen masa tambayoyi nan da ranar Laraba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Dole tsohuwar Ministar jin-kai da cigaban al’umma, Sadiya Umar-Farouq, ta bayyana a hedikwatar hukumar EFCC.

EFCC mai yaki da masu rashin gaskiya ta dage a kan yi wa Sadiya Umar-Farouq tambayoyi, The Nation ta kawo rahoton.

EFCC - Sadiya Umar-Farouq
EFCC tana neman Hajiya Sadiya Umar-Farouq CON Hoto: @Sadiya_farouq
Asali: Twitter

"Hajiya Sadiya Umar-Farouq ba ta da lafiya"

Kara karanta wannan

Sadiya Umar ta kawo kanta ba tare da bata lokaci ba, EFCC

Tsohuwar ministar tarayyar ta bada uzurin rashin lafiya a matsayin abin da ya hana ta amsa goron gayyatan da aka aika mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa dukkan alamu Hukumar ta EFCC ba ta karbi wannan uzuri ba, ta kuma ki amincewa da bukatar lauyan Sadiya Umar-Farouq.

EFCC ta ki ba Sadiya Umar-Farouq kwana 21

Hajiya Sadiya Umar-Farouq ta hannun lauyanta, ta bukaci a tsawaita mata wa’adin da makonni uku, amma ba tayi nasara ba.

Hukumar EFCC ta ce ya zama dole ‘yar siyasar ta zo hedikwatarta da ke birnin Abuja domin ayi mata tambayoyi nan da kwanaki uku.

Majiya ta fadawa jaridar ba za a iya jiranta na tsawon makonni uku ba, dole ta amsa gayyatar cikin kwana uku ko a dauki mataki.

Kamar yadda labari ya zo, a wasikar da ta rubutawa EFCC, a ranar Laraba Sadiyar Farouk ta nemi karin lokaci domin kula da lafiyarta.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: Ministar Buhari ta bayyana babban dalilin kin amsa gayyatar EFCC, ta tura bukata 1

Babu dalilin jin tsoron EFCC

Wani ma’aikaci ya ce da zuwan Ola Olukoyede, za ka iya zuwa ofishin EFCC, ka kwana a gidanka a ranar ba tare da an tsare ka ba.

EFCC ta na jiran ‘yar siyasar a hedikwatarta, ta ce za a tanada mata likita idan ta kama.

Takardar da aka ba lauyanta ta nuna ana bukatar ganinta a ranar Laraba da karfe 10:00 na safe kamar yadda doka ta bada dama.

Za a iya kamo Sadiya Umar-Farouq

Ana ji matakin da jami’an hukumar za su dauka shi ne su nemi jami’an tsaro su cafko ta.

Tsohuwar ministar kasar za ta zauna da jami’an da ke binciken abubuwan da su ka faru a lokacin da ta ke ofis tsakanin 2019 da 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng