Hukumar EFCC Ta Ayyana Neman Minista a Mulkin Buhari, Sadiya Farouq Ruwa a Jallo
- Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dukiyar kasa
- A wata sanarwa da ta fitar, EFCC ta ce wuri na karshe da aka ga Sadiya shi ne a Abuja, inda ta roki 'yan Najeriya su kai rahoto idan sun ganta
- A ranar 16 ga Afrilu, 2026, babbar kotun tarayya da ke Apo, Abuja ta bayar da sammacin kama Sadiya bayan ta ki halartar zaman kotu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta ayyana tsohuwar Ministar Harkokin Jin Ƙai da Yaki da Talauci, Hajiya Sadiya Umar Farouq, a matsayin wadda take nema ruwa a jallo.
Hukumar EFCC ta ayyana neman Sadiya Farouk ruwa a jallo bisa zargin amfani da ofis ba daidai ba da karkatar da kuɗin gwamnati da suka kai biliyoyin Naira.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Instagram yau Asabar, 9 ga watan Mayu, 2026.
Hukumar EFCC ta buƙaci duk wanda ke da bayanai kan inda tsohuwar ministar take da ya tuntubi ofisoshinta da ke kusa da shi a faɗin ƙasar nan ko ta lambobin wayar da aka bayar.
Dalilin EFCC na neman Sadiya Farouq
A cewar EFCC, Sadiya Umar Farouq mai shekaru 52 ’yar asalin jihar Zamfara ce, kuma adireshinta na ƙarshe da aka sani shi ne EN008, Okpo River, kusa da titin Agulu, Maitama, Abuja.
Tsohuwar ministar ta yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Hukumar EFCC na binciken zargin badakalar kuɗi da ya kai kusan Naira biliyan 37 da ake alaƙantawa da ma’aikatar harkokin jin kai a lokacin mulkinta.
Kotu ta bayar da umarnin kama ta
A ranar 16 ga Afrilu, 2026, babbar kotun tarayya da ke Apo, Abuja ta bayar da sammacin kama Sadiya Umar Farouq bayan ita da sauran waɗanda ake tuhuma sun gaza bayyana a gabanta domin fara shari’a.
Mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya kuma bayar da umarnin kama Bashir Nura Alkali, babban sakatare a ma’aikatar jin kai na wancan lokaci.
An bayar da umarnin ne bayan EFCC ta nemi hakan saboda waɗanda ake tuhuma ba su halarci zaman kotun da aka shirya domin gurfanar da su ba.

Source: Facebook
Zarge-zargen da ke kan Sadiya Farouq
Sadiya Umar Farouq, Bashir Nura Alkali da wani Sani Mohammed na fuskantar tuhume-tuhume guda 21 da suka shafi karya amana da kuma amfani da ofis ba bisa ka’ida ba.
EFCC ta yi zargin cewa sun wawure kusan Dala miliyan 1.3 da kuma Naira miliyan 746.6 da aka ware domin shirye-shiryen gwamnati, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
EFCC na tsare da wasu malamai a Najeriya
A baya, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC na kasa, Ola Olukoyede ya ce sun kama malaman addinin musulunci da limaman coci kan zargin zamba.
Ya kuma bayyana cewa tuni aka yanke wa wasu daga cikin malaman da EFCC ta cafke hukunci bayan gurfanar da su a gaban kotu, wasu kuma suna nan tsare.
Olukayode ya ce aikata laifuffakan cin hanci da rashawa bai takaita kan 'yan siyasa kadai ba, akan samu irin hakan a kungiyoyin addini a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

