Abin Tausayi: Malamin Addini da Matarsa Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Ruwa

Abin Tausayi: Malamin Addini da Matarsa Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Ruwa

  • An shiga yanayi mara dadi sakamakon kifewar wani jirgin ruwa wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma
  • Majiyoyi sun ce wasu mutane biyu har da fasto da matarsa sun mutu bayan kwale-kwalen ya kife a ruwa
  • An ceto wasu daga cikin fasinjojin jirgin, yayin da aka gano gawar matar faston, ana ci gaba da neman faston da sauran ɓatattun mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Odioma, Beyelsa - Rundunar ’yan sanda da matasan Odioma sun tabbatar da hatsarin jirgin ruwa a wani kogi da ke yankin a jihar Bayelsa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hukumomi sun tura jami’an ruwa da masana harkar ruwa domin gudanar da aikin ceto.

An rasa rayuka a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
Taswirar jihar Bayelsa da aka samu hatsarin jirgin ruwa. Hoto: Legit.
Source: Original

Fasto da matarsa sun mutu a hatsari

Wani fasto da matarsa sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da mambobin coci ya kife a kogin Odioma-Brass da ke Bayelsa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yahudawa sun bankawa masallaci, motoci wuta yayin ibada a Isra'ila

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi da mummunan yanayin iska a yankin.

Majiyoyi sun ruwaito cewa kwale-kwalen na kan hanyarsa zuwa Yenagoa domin halartar wani shirin coci lokacin da hatsarin ya afku a ruwa.

An ce an samu nasarar ceto wasu daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin, amma faston da matarsa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Daga baya an gano gawar matar faston tare da kai ta ɗakin ajiye gawa, yayin da ake ci gaba da neman faston da sauransu.

Yan sanda sun kai dauki da aka yi hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
Sufeta-janar na ƴan sandan Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Martanin rundunar ƴan sanda kan hatsarin

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Bayelsa, DSP Musa Mohammed, ya tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin ruwan ga manema labarai ranar Asabar 16 ga watan Mayun 2026.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a tantance yawan waɗanda suka mutu ba saboda jami’an ceto na ci gaba da gudanar da bincike a yankin, cewar Sahara Reporters.

Mohammed ya ce sashen ruwa na rundunar ’yan sandan Najeriya ya shiga aikin ceto domin taimakawa wajen gano tare da ceto sauran fasinjojin da suka ɓace.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa malamin addinin Musulunci daurin rai da rai a Birtaniya

Shugaban matasan Odioma, Moses Inene, shi ma ya tabbatar da cewa faston da matarsa suna cikin waɗanda hatsarin ya shafa a kogin.

A cewarsa, an tattara masana harkar ruwa a yankin domin taimaka wa aikin bincike da ceto, yayin da ake fatan gano sauran mutanen lafiya.

Inene ya ce an riga an gano gawar matar faston, amma har yanzu ana ci gaba da neman faston da sauran mutanen da suka ɓace.

Mutane 60 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

A baya, an ji cewa a ranar Laraba, 3 ga watan Satumba, 2025 aka samu labarin kifewar wani jirgin ruwa bayan ya dauko mutane kusan 100 a jihar Niger.

Hatsarin jirgin ya rutsa da mata da yara, wadanda aka gano cewa suna hanyar zuwa ta'aziyyar rasuwa ne a karamar hukumar Borgu.

Shugaban karamar hukumar Borgu ya ce adadin wadanda suka mutu a hatsarin ya karu daga mutane 29, yanzu sun kai akalla mutum 60.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.