Gwamnatin Zamfara Ta Magantu da Ake Zargin Harin Jirgi Ya Kashe Yan Kasuwa 100
- An samu ce-ce-ku-ce bayan harin saman da rundunar sojin saman Najeriya ta kai kasuwar Tumfa a jihar Zamfara
- Majiyoyi suka ce mazauna yankunan sun tabbatar da cewa kusan mutum 100 sun mutu sakamakon harin jirgin da aka kai
- Sun bayyana cewa mata da yara sun fi yawa cikin wadanda suka mutu, yayin da gwamnati ta dage cewa yankin maboyar ‘yan bindiga ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zurmi, Zamfara - Rikici ya biyo bayan harin saman da aka kai kasuwar Tumfa da ke karamar hukumar Zurmi a Zamfara.
An tabbatar da cewa mazauna yankin sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu yayin harin.

Source: Original
Ana zargin rundunar sojin saman Najeriya da kai harin ranar Lahadi 9 ga watan Mayun 2026 yayin da kasuwar ke cike da masu saye da sayarwa, cewar Leadership.
Abin da mazauna Zamfara ke cewa
Wani mazaunin yankin da ya yi magana da harshen Hausa ta wayar tarho ya ce harin ya afku ba tare da gargadi ba.
Ya bayyana cewa mafi yawan wadanda suka mutu mata ne, domin su ne suka fi yawa cikin ‘yan kasuwar da suka halarta.
Mazaunin ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa manyan asibitocin Zurmi da Kaura Namoda domin samun kulawa ta musamman.

Source: Twitter
Martanin gwamnatin Zamfara kan 'harin'
A gefe guda, gwamnatin Zamfara ta ce yankin da aka kai harin sanannen maboyar ‘yan bindiga ne da jami’an tsaro ke bibiyarsu.
Mai ba gwamnan Zamfara shawara kan harkokin tsaro, Ahmed Danmanga, ya ce gwamnatin jihar ba ta san akwai kasuwa a yankin ba.
Shugaban karamar hukumar Zurmi, Hon. Samaila Hussaini Moriki, ya ce ana gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa kauyen Tumfa na daga cikin wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga da rikice-rikicen tsaro a Zamfara.

Kara karanta wannan
"Yara na 3 sun mutu," Magidanci ya sabawa bayanin sojoji kan kuskuren jefa bam a Neja
Rahoton ya bayyana cewa wannan ne karo na biyu cikin wata guda da harin sama ya afkawa kasuwa mai cike da jama’a.
Amnesty Int'l ta yi magana kan harin
Kungiyar Amnesty International ta ce akalla fararen hula 100 ne suka mutu a harin, tare da bukatar gudanar da bincike cikin gaggawa.
Kungiyar ta bayyana cewa mata da yara mata na daga cikin wadanda suka mutu, yayin da wasu da dama ke kwance a asibitoci, cewar Daily Post.
Amnesty International ta ce jiragen yaki sun fara shawagi kan yankin kafin daga bisani su dawo suka kai harin kan kasuwar Tumfa.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta zargi jami’an tsaro da nuna rashin kula da rayukan fararen hula yayin yakar ‘yan bindiga da masu tada kayar baya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin da ya faru ba.
Sojoji sun kashe jagoran yan ta'adda
An ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun kai hare-hare kan wani wuri da 'yan ta'adda ke gudanar da taro a jihar Zamfara.
Sojojin saman sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama ciki har da jagororinsu bayan sun yi masu ruwan wuta.
A cewar sanarwar da aka fitar, an kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri wadanda suka tabbatar da cewa jagororin 'yan ta'addan na gudanar da taro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

