Matashi 'Dan 37 da Wasu Masu Kananan Shekaru da ke Neman Kujerar Gwamnan Osun

Matashi 'Dan 37 da Wasu Masu Kananan Shekaru da ke Neman Kujerar Gwamnan Osun

Ɗan takarar YPP, Olalekan Ogunsakin mai shekaru 37, shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin ’yan takarar gwamnan Osun na 2026, inda aka samu matasa suna neman kujerar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun –Aƙalla ’yan takara uku mafi ƙarancin shekaru da ke neman kujerar gwamnan Jihar Osun a zaɓen 2026 ba su kai shekaru 40 ba.

Mafi ƙarancin shekaru a cikinsu yana da shekaru 37, yayin da ƙananan jam’iyyun siyasa ke amfani da matasa wajen neman kalubalantar manyan jam’iyyun siyasa a jihar.

Matasa uku sun shiga ana fafatwa da su a zaben Osun
Olalekan Ogunsakin da Adeyemi Adesina Doro masu neman kujerar gwamnan Osun Hoto:OgunsakinOlaleka/Adesina O. Adeyemi-Dora
Source: UGC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa akalla akwai yan takara 15 da ake fafatawa da su a zaben gwamnan jihar Osun wanda ake gudanarwa a wannan rana ta Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Matan da aka gani sun fito neman kujera a zaben gwamnan Osun

Yan takara masu karanin shekaru a Osun

Jaridar Punch ta kawo cewa daga cikin masu neman takarar gwamna a jihar Osun akwai Olalekan Ogunsakin na YPP, Olajide Esan AAC da sauran yan takara.

Amma masu karancin shekaru a cikinsu sun hada da:

1. Olalekan Ogunsakin

Olalekan Ogunsakin mai shekaru 37 shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin mutane uku da aka gano su ne masu kananan shekaru a zaben ranar Asabar.

Yana takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar YPP, kuma yana cikin ’yan takarar ƙananan jam’iyyun da ke neman lashe kujerar gwamnan jihar.

2. Olajide Esan

Olajide Esan, mai shekaru 39, yana neman kujerar gwamnan Osun ne a ƙarƙashin jam’iyyar AAC a zaben da ya dauki zafi na yau 15 ga watan Agusta, 2026.

Yana da takardar shaidar kammala makarantar firamare, da takardar kammala sakandare, sannan yana da digiri. Abokin takararsa shi ne Bello Muideen Yekeen, mai shekaru 51.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Jerin manyan yan takarar gwamna 14, jam'iyyu, shekaru da matakin karatunsu

3. Adeyemi-Doro Adesina

Adeyemi-Doro Adesina mai shekaru 39 shi ne ɗan takarar gwamnan Osun na jam’iyyar APGA, kafin daga bisani ya janye daga takarar.

Matashi mai shekaru 39 ya shiga cikin masu neman kujerar gwamna Ademola Adeleke
Adesina O. Adeyemi-Dora, mai neman takarar kujerar gwamnan Osun Hoto: Prince Adesina O. Adeyemi-Dora
Source: Facebook

A ranar Asabar, 8 ga Agusta, ya sanar da janyewarsa daga takarar tare da bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar jam’iyyar APC.

Da yake magana a shirin The Morning Brief na Channels Television ranar Litinin, 10 ga Agusta, Adesina ya ce shawarar tasa ta samo asali ne daga abin da ya yi imanin shi ne mafi alheri ga Jihar Osun da al’ummarta.

Ya kuma bayyana dalilan da suka sa ya shiga takarar, kafin daga bisani ya sauya matsayinsa tare da mara wa ɗan takarar APC baya.

An cafke dan majalisa a Osun

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta ce jami’an FBI-IRT sun kama dan majalisar dokokin Jihar Osun mai wakiltar Irewole/Isokan, Abiola Ibrahim, a Ikire ana zabe a yankin.

Kara karanta wannan

An tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC yayin da ake shirin zaben gwamnan Osun

An kama dan majalisar ne tare da wasu mutane kusan 146 da ake zargi da kasancewa ‘yan amshin shata a ranar zaben gwamnan jihar kuma ana zargin an so a yi amfani da su ne yayin kada kuria.

Dan majalisar ya musanta daukar mutanen, yana mai cewa mutanen da aka samu a gidansa masu kada kuri’a ne da suka zo domin kada kuri’a a zaben da zai tabbatar wa da Osun sabon gwamnan ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng