Sojojin Sama Sun Hallaka Jagororin 'Yan Ta'adda a Zamfara bayan Yi Masu Ruwan Wuta

Sojojin Sama Sun Hallaka Jagororin 'Yan Ta'adda a Zamfara bayan Yi Masu Ruwan Wuta

  • Dakarun sojojin sama na Najeriya sun kai hare-hare kan wani wuri da 'yan ta'adda ke gudanar da taro a jihar Zamfara
  • Sojojin saman sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama ciki har da jagororinsu bayan sun yi masu ruwan wuta
  • A cewar sanarwar da aka fitar, an kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri wadanda suka tabbatar da cewa jagororin 'yan ta'addan na gudanar da taro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Dakarun haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma sun karkashe ’yan ta’adda da dama a jihar Zamfara.

Sojojin sun hallaka tsagerun ne yayin wani harin sama da aka kai a wurin taron jagororin ’yan ta’adda a jihar Zamfara.

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a Zamfara
Jiragen yakin sojojin sama na Najeriya na shawagi Hoto: Sodiq Adelakun
Source: Getty Images

Jaridar The Punch ta ce an bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Ana fargabar sabon harin sojoji ya kashe mutanen gari a jihar Neja

Sojoji sun kashe jagororin 'yan ta'adda

Aikin sojojin, wanda aka gudanar ranar 10 ga Mayu, 2026, ya biyo bayan abin da sojoji suka bayyana da ingantattun bayanan sirri da ke nuna gudanar da wani babban taro na shahararrun jagororin ’yan ta’adda da kwamandoji daga sassan yankin Afirka ta Yamma.

A cewar sanarwar, rahotannin sirri sun tabbatar da cewa ’yan ta’addan sun taru ne a wani boyayyen wuri a ƙauyen Tumfa da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Sojojin sun ce wurin taron "wasu gine-gine ne da ke gefen Arewacin ƙauyen" kuma an ɓoye shi a cikin wani yanki mai duhun ciyayi, wanda manyan bishiyoyin mangwaro suka kare a gefen wani rafi.

An farmaki wurin taron 'yan ta'adda

Sanarwar ta ƙara da cewa taron an shirya shi ne da nufin tsara hare-hare da ayyukan ta'addanci da nufin cutar da al'ummomin da ba su ji ba, ba su gani ba a yankin Arewa maso Yamma, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan ta'adda kwanton bauna a Katsina, an kashe tsageru

Sanarwar ta ce sashen 'Sector 2' na Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar dakarun sojojin sama, sun kai harin sama kan maɓoyar ’yan ta’addan da aka gano, bayan sun yi gaggawar ɗaukar mataki kan bayanan sirrin da aka samu.

"Harin ya yi nasarar ruguje ginin, wanda shi ne wurin taron ’yan ta’addan."

- Laftanar Kanar Aliyu Danja

Sojojin sama sun hallaka jagororin 'yan ta'adda a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi wa 'yan ta'adda barna

Sanarwar ta ƙara da cewa tantance barnar da aka yi bayan fafatawar ya tabbatar da cewa an kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da sauran waɗanda suka tsira suka tsere daga yankin cikin ruɗani.

Sojojin sun ƙara bayyana cewa ƙarin sintiri ta sama da bayanan sirri sun nuna motsin wasu da ake zargi abokan tafiyar ’yan ta’addan ne da ke ƙoƙarin kwashe gawarwaki da waɗanda suka ji rauni daga wurin.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi kazamin artabu da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

An kashe sojoji biyu yayin da suke fatattakar wani hari da mayakan 'yan ta’adda na ISWAP suka kai a wani sansanin sojoji da ke Magumeri a jihar Borno.

Hakazalika, sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama tare da kwato makamai daga hannunsu yayin artabun da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng