Lokuta 13 da 'Yan Ta'adda Suka Farmaki Sansanonin Sojoji a Farkon 2026

Lokuta 13 da 'Yan Ta'adda Suka Farmaki Sansanonin Sojoji a Farkon 2026

FCT, Abuja - A watan Janairun 2025, Shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunonin tsaro da su kai yaƙi har sansanonin ’yan fashin daji da na ’yan ta’adda, musamman a shiyyar Arewa maso Yamma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Umarnin shugaban kasar ya biyo bayan harin ranar 4 ga Janairu da aka kai wani sansanin sojoji da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji shida.

'Yan ta'adda sun farmaki sansanonin sojoji
Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta tattaro lokutan da 'yan ta'adda suka farmaki sansanonin sojoji a watannin farko na shekarar 2026.

'Yan ta'adda sun farmaki sansanonin sojoji

Sai dai maimakon kai yaƙin sansanonin ’yan tawayen, a shekarar 2026, ’yan ta'addan ne suka nuna kamar sun sauya salon yaƙin.

'Yan ta'addan suna kai hare-hare kai tsaye ga rundunonin sojoji ta hanyar amfani da dabarar da suka kira “ƙone sansanoni” wani shiri na musamman da nufin raunana ƙarfin dakarun tsaro ta hanyar kai hari kan sansanonin sojoji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki fadar basarake yayin harin ramuwar gayya a Zamfara

Lokutan da aka farmaki sansanonin sojoji

Tun watan Janairu, aƙalla sansanoni 13 a faɗin Najeriya, musamman a Borno, aka kai wa hari, lamarin da ke nuna sauyi a dabarun yaƙi da ƙarfin maharan.

Ga jerinsu a nan kasa:

1. 4 ga Janairu, (Sabon Gari, Borno)

'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki sansanin dakarun sojoji da ke Sabon Gari a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Hedkwatar tsaro a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa dakarun sojoji shida suka rasa rayukansu sakamakon harin.

Hakazalika ta bayyana cewa an kashe 'yan ta'addan ISWAP 34 tare da kwato makamai da dama a hannunsu.

2. 16 ga Janairu (Borno da Adamawa)

A ranar 16 ga Janairu, rundunar sojojin kasa ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun dakile wasu hare-hare da aka shirya wa sansanonin soji a jihohin Adamawa da Borno.

S.A. Atokolo, muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar, ya ce ’yan ta’addan sun fara ƙoƙarin ƙwace wani sansanin sintiri ne a Sabon Gari, ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa amma dakarun sokoji suka fatattake su.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa asibiti a Neja, babban likita ya fada hannun miyagu

Haka kuma an dakile wani harin daban da aka kai sansanin sojoji na Azir da ke Borno bayan kwashe lokaci ana fafatawa da taimakon jiragen yaƙi, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

3. 20 ga Janairu (Damasak, Borno)

Wasu mayakan ƙungiyar 'yan ta'adda ta IWAP sun kai hari kan tawagar sojoji kusan 30 daga sansanin Damasak.

Jaridar Vanguard ta ce wani Janar (Manjo Janar) da ke jagorantar sintirin ya riga mu gidan gaskiya tare da wasu sojoji a yayin harin.

Wannan lamari ya nuna haɗarin da ke akwai ga dakarun da ke yawo da kuma waɗanda aka jibge a sansanoni.

4. 29 ga Janairu, (Sabon Gari, Borno)

Wasu ’yan ta'adda sun kai hari da sanyin safiya a sansanin sojoji na Sabon Gari a jihar Borno, tashar Reuters ta kawo rahoton.

Maharan, waɗanda aka ba da rahoton cewa sun yi amfani da jirage marasa matuƙa, sun lalata motocin sojoji da dama.

Rundunar sojoji ta tabbatar da asarar rayukan sojoji da mambobin jami’an sa-kai (Civilian JTF), amma ba ta bayyana adadi ba.

5. 3 ga Maris, (Ngoshe, Borno)

Kara karanta wannan

Ba sauki: Sojoji sun kashe babban kwamandan ISWAP da 'yan ta'adda da dama

Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hare-hare daga sama bayan wani yunƙurin kai hari kan sansanonin sojoji a Ngoshe.

Majiyoyi daga bangaren sojoji sun bayyana cewa an kashe fiye da mambobin Boko Haram/ISWAP su 50.

6. 9 ga Maris (Kukawa, Borno)

Wani babban jami’in soja ya kwanta dama lokacin da ake zargin mayakan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Kukawa.

A cewar Zagazola Makama, wata kafar yaɗa labarai da ke mayar da hankali kan yankin Tafkin Chad, dakarun sun gwabza da ’yan tawayen inda aka samu asarar rayuka a ɓangarorin biyu.

7. 10 ga Maris, (Doron Baga, Borno)

Ba a cika sa’o’i 24 da harin Kukawa ba, ’yan tawayen sun sake kai hari a Borno, inda suka farmaki sansanin sojoji a Doron Baga.

Dakarun sojoji sun samu nasarar dakile harin 'yan ta'addan bayan kwashe kusan sa’a ɗaya ana fafatawa da makamai.

8. 13 ga Maris, (Bama, Borno)

Sojoji sun dakile harin mayakan ISWAP bayan wani yunƙurin ƙwace sansanin soji a Banki, ƙaramar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki mataki kan hare haren Boko Haram da suk kashe manyan sojojin Najeriya

An dakile harin ne da taimakon rundunar sojojin sama (NAF), inda aka ce ’yan tawayen sun tsere a guje.

9. 18 ga Maris, (Malam Fatori, Borno)

Dakarun Operation Hadin Kai, tare da tallafin sojin sama, sun dakile yunƙurin 'yan ta'adda na shiga wani sansanin sojoji.

Maharan sun taho ne a ƙasa sannan suka turo jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai. Rundunar sojin ta ce an kashe aƙalla ’yan ta'adda 61.

10. 28 ga Maris, (Mandaragirau, Borno)

Mambobin Boko Haram/ISWAP sun yi yunƙurin ƙwace sansanin soji a Mandaragirau, ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno.

Sai dai dakarun sojoji sun fatattaki 'yan ta'addan inda suka kashe takwas daga cikinsu har lahira biyo bayan harin.

Sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

11. 9 ga Afirilu, (Benisheikh, Borno)

Sansanin sojojin Najeriya da ke Benisheikh a Borno ya fuskanci harin 'yan ta'adda da misalin ƙarfe 12:30 na dare.

Babban kwamandan sansanin, Birgediya Oseni Braimah, tare da wani jami’in daban da sojoji biyu sun rasa rayukansu a harin, jaridar The Punch ta kawo labarin.

12. 13 ga Afirilu, (Monguno, Borno)

Kara karanta wannan

Ba Sassauci: Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan 'yan ISWAP, an kashe tantirai masu yawa

Wani Kanar da sojoji shida ne aka kashe a ranar 13 ga Afrilu lokacin da ’yan ta'adda suka kai hari kan dakarun sojoji a wurin da ake kira Charlie 13.

Kwamandan da mutanensa sun fito ne don mayar da martani kan harin da aka kai wani sansanin sojoji a Monguno da daddare.

13. 20 ga Afirilu, (Kemanji, Kwara)

Sojoji uku ne suka mutu a ranar Litinin bayan da ’yan ta’adda suka kai hari wani sansanin soji a garin Kemanji da ke ƙaramar hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, ya ce dakarun sun kashe ’yan ta’adda da dama sannan sun tabbatar da cewa ba a yi garkuwa da kowa ba.

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan ISWAP ciki har da kwamandansu.

Sojojin sun kashe wani babban kwamandan ISWAP da aka bayyana sunansa da Abu Umar Bundi Munzir tare da wasu ‘yan ta'adda 24 a jihar Borno.

Nasarar sojojin ta biyo bayan dakile wani harin haɗin gwiwa da aka kai wa kauyen Kukareta da ke Borno da dakarun Operation Hadin Kai suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng