Hajjin Bana: Maniyyaciya daga Taraba Ta Rasu Awanni Kadan kafin Tafiya Saudiyya
- An shiga jimami bayan rasuwar daya daga cikin maniyyatan da suka fito daga jihar Taraba kafin su tashi zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana
- Maniyyaciyar wadda ta fito daga jihar Taraba ta rasa ranta ne awanni kadan kafin jirginsu ya tashi daga birnin Yola zuwa kasar Saudiyya
- Tuni aka yi wa marigayiyar jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Yola bayan samun amincewar danginta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Yola, jihar Adamawa - Wata mata mai niyyar gudanar da aikin Hajji daga jihar Taraba ta rasu a Yola, jihar Adamawa, sa’o’i kaɗan kafin tashinsu zuwa ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026.
Marigayiyar, wadda aka bayyana sunanta a matsayin Hajiya Dado Hammadu ta fito ne daga ƙaramar hukumar Sardauna ta jihar Taraba.

Source: Twitter
Jami’in yaɗa labarai na hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Taraba, Hamza Baba Muri, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Maniyyaciya daga Taraba ta rasu a Yola
An bayar da rahoton cewa ta kamu da rashin lafiya jim kaɗan bayan isarta filin jirgin sama na kasa da kasa na Yola tare da sauran maniyyatan da ke jiran jigilarsu zuwa Saudiyya.
Hamza Baba Muri ya ce marigayiya Dado Hammadu ta fara rashin lafiya ne a daren Lahadi, 10 ga watan Mayun 2026 inda aka garzaya da ita zuwa babban asibitin tarayya (FMC) na Yola, inda ta rasu sa’o’i kaɗan bayan isarta.

Kara karanta wannan
Masu neman takara 6 sun hakura, an bar wa Shekarau tikitin sanatan Kano ta Tsakiya
An yi wa marigayiyar jana'iza
A cewar jami'in yada labaran, binciken likitoci sun gudanar ya nuna cewa tana fama da matsalar karancin bugawar jini.
Hamza Baba Muri ya bayyana cewa an binne marigayiyar a Yola ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026 da safe bayan samun amincewar danginta, rahoton Sahelreporters ya tabbatar da hakan.

Source: Original
Babu rabon marigayiyar za ta je Saudiyya
Ya ƙara da cewa marigayiyar tana ɗaya daga cikin maniyyata 415 da aka tsara za su tashi a rukunin farko na jihar Taraba don aikin Hajjin 2026 ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2026.
A cewarsa, sallar jana’izar ta samu halartar mashawarci na musamman ga gwamna kan Al’amuran Alhazai, Alhaji Hamman’Adama Tukur, shugaban kwamitin filin jirgin Sama na Yola, Malam Jamal Abdul’nasir; ma’aikatan hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Taraba; da kuma ɗimbin maniyyata da aka shirya za su tashi a jirgin farko.
Hukumar NAHCON ta fara jigilar maniyyata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON), ta fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 da jigilar maniyyata 474 daga jihar Kogi zuwa kasa mai tsarki watau Saudiyya.
An gudanar da bikin ƙaddamar da jigilar maniyyatan ne a birnin Abuja bayan an sauya wajen taron daga jihar Ogun, inda jami’ai da sarakuna suka halarta.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abba Yusuf ya gargadi maniyyata kan karya dokokin hajji, yana mai cewa hukumomin Saudiyya suna ɗaukar matakan hukunci masu tsauri kan masu sabawa ƙa’idoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

