Jirgin Sama Dauke da Wasu Manyan Mutane Ya Gamu da Matsala a Hanyar zuwa Katsina
- Wani jirgin sama na kamfanin Max Air da ya tashi daga birnin tarayya Abuja zuwa jihar Katsina ya gamu da matsalar inji a sararin sama
- Fasinjoji sun shiga yanayin tashin hankali bayan jirgin saman ya fara sauka ba zato ba tsammani, inda ya koma Abuja cikin gaggawa
- Wata fasinja ta ce jirgin ya fara sauka cikin minti 10 bayan tashi, lamarin da ya jawo jinkiri ga fasinjojin da suka nufi Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani jirgin kamfanin Max Air da ya taso daga Abuja zuwa Katsina ya samu matsalar inji jim kadan bayan tashinsa daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe.
Wata fasinja da ta bayyana yadda lamarin ya faru ta ce jirgin ya samu matsalar ne kusan minti 10 bayan tashinsa daga Abuja, inda ya fara sauka cikin gaggawa kamar zai fado.

Kara karanta wannan
"Babu hujja," Sojojin Najeriya sun yi magana kan zargin kashe fiye da mutane 100 a Zamfara

Source: Facebook
Abin da ya garu da jirgin Max Air
A wani bidiyo da Nafiu Muhammad ya wallafa a shafin X, an ga fasinjoji suna tsaye a harabar filin jirgi bayan jirgin ya sauka lafiya a Abuja.
Fasinjar ta ce:
“Muna filin jirgi yanzu bayan wani abin firgici da ya faru da jirgin Max Air daga Abuja zuwa Katsina. Kusan minti 10 bayan tashi, sai aka samu wata matsala da ta sa jirgin ya fara sauka da sauri kamar yana fadowa.
“Matukan jirgin sun yi nasarar dawo da shi daidai sannan suka mayar da shi Abuja domin tsaronmu. Mun sauka lafiya amma har yanzu muna tsaye a filin jirgi ba tare da sanin abin da zai biyo baya ba.”
Manyan mutane na cikin jirgin saman
Fasinjar ta ce akwai manyan mutane a cikin jirgin ciki har da Abba, dan attajirin dan kasuwar nan, Dahiru Mangal, mai taimaka wa gwamnan Katsina kan harkokin kafafen sada zumunta da wasu jami’an gwamnati.
Ta ce har yanzu ba su san ko za a gyara jirgin su ci gaba da tafiya da shi ko kuma za a samar musu da wani jirgin ba.
“Har yanzu muna tsaye a waje kuma muna jin kamar an bar mu babu taimako. Ku ci gaba da yi mana addu’a,” in ji ta.
Kamfanin Max Air ya tabbatar da lamarin
A wata sanarwa da kamfanin Max Air ya fitar ranar Talata, ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da jirgin VM1620 mai zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Katsina.
Kamfanin ya ce bayan kusan minti 15 da tashin jirgin Boeing 737-300 mai lamba 5N-DAB, ma’aikatan jirgin sun lura da wata matsalar inji.
“Bisa tsarinmu na tsaro da dokokin zirga-zirgar jiragen sama, matukan jirgin sun yanke shawarar dawo da shi Abuja nan take. Jirgin ya sauka lafiya kuma dukkan fasinjoji da ma’aikata sun fita lafiya,” in ji sanarwar.
Max Air ya ce tuni ya tura wani jirgi mai lamba 5N-DMK daga Kano zuwa Abuja domin ci gaba da jigilar fasinjoji zuwa Katsina da sauran wurare, kamar yadda The Cable ta kawo.

Kara karanta wannan
Sheikh Sani Khalifa ya amayar da abin da ya sani kan shirin juyin mulki a gaban kotu

Source: Getty Images
Kamfanin Rano Air ya dakatar da aiki
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin jiragen sama na Rano Air ya sanar da dakatar da aiki a wasu daga cikin hanyoyin zirga-zirgarsa na wucin gadi.
Ya ce hauhawar farashin man jiragen sama ya sa gudanar da sufuri zuwa wasu jihohi ya zama mai matuƙar wahala da rashin riba.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa hanyoyin Maiduguri da Gombe na daga cikin waɗanda ake tunanin za a dakatar na ɗan lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
