Yadda aka Kashe Man Jirgi Yana Sama, Ya Fado Mutane 132 Suka Mutu
- Rahotanni sun nuna cewa hatsarin jirgin China a 2022 da ya jawo mutuwar mutane 132 ya faru ne bayan an katse masa man fetur yana sararin sama
- Binciken hukumar NTSB ya nuna cewa an katse maballan man fetur na injunan jirgin yayin da yake tafiya, abin da ya sa ake zargin an yi sakaci
- Har yanzu kasar China ba ta fitar da cikakken rahoto game da hadarin ba, sai dai bincike na cigaba kan yiwuwar gano wasu dalilan faruwar hadarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
China - An fitar da rahoto kan wani jirgin sama na Boeing 737 da ya fadi a wani tsauni a kasar China a shekarar 2022, inda ya kashe mutane 132 da ke cikinsa.
Rahotanni sun nuna cewa an katse masa man fetur ne yayin da ya ke tafiya, kamar yadda sababbin bayanai daga Hukumar Tsaron Sufurin Amurka (NTSB) suka nuna.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa binciken NTSB ya nuna cewa an katse maballan mai na dukkan injunan jirgin kamfanin yayin da yake sama.
Labari kan hadarin jirgin China
An bayyana cewa hatsarin ne mafi muni a kasar China cikin shekaru da dama, duk da cewa musabbabin lamarin ya dade yana zama abin al’ajabi.
Har yanzu kasar China ba ta fitar da cikakken rahoto kan lamarin ba, tana mai danganta hakan da batutuwan tsaron kasar.
Rahoton NTSB, wanda aka fitar karkashin dokar neman bayanai ta FIO, ya ce saurin injunan jirgin ya ragu bayan rufe maballan man fetur.
Maballan man fetur su ne na’urorin da ke sarrafa yadda mai ke shiga injunan jirgi, kuma matuka jirgi na amfani da su wajen kunnawa ko kashe injuna.
Sababbin bayanan da aka fitar sun fito ne daga daya daga cikin wasu na’urorin jirgin, wadanda ke daukar dukkan muhimman bayanan aiki.
Rahoto ya bayyana cewa an dauko na’urar daga tarkacen jirgin sannan aka kai ta dakin bincike na NTSB a Washington DC domin nazari.

Source: Getty Images
Yaushe jirgin ya yi hadari a China?
A watan Maris na 2022, jirgin ya tashi daga birnin Kunming, babban birnin lardin Yunnan, kuma ana sa ran zai sauka a Guangzhou.
An bayyana cewa jirgin ya kwashe sama da awa guda a sararin sama kuma yana dab da isa inda zai sauka ne kafin ya fadi.
Saboda lamarin ya faru a China kuma ya shafi jirgin kamfanin kasar, Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta China (CAA) ce ta jagoranci binciken.
CNN ta wallafa cewa masu bincike sun yi la’akari da dalilai daban-daban da ka iya jawo hatsarin, ciki har da yiwuwar an fado da shi kasa ne da gangan, kuskuren matuki, ko matsalolin fasaha ko karo a sararin sama.
Jirgin Colombia ya yi hadari
A wani labarin, mun kawo muku cewa wani jirgin sojojin kasar Colombia dauke da dakaru sama da 100 ya yi hadari yayin da yake tafiya.
Ministan tsaron kasar, Pedro Sánchez ya tabbatar da faduwar jirgin saman tare da yin karin haske kan mutanen da suka jikkata.
Shugaban kasar Columbia, Gustavo Petro ya yi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, inda ya ce an mayar da hankali kan wadanda suka ji rauni.
Asali: Legit.ng


