Hukumar JAMB Ta Sanya Ranar da Za Ta Saki Sakamakon Jarabawar UTME 2026

Hukumar JAMB Ta Sanya Ranar da Za Ta Saki Sakamakon Jarabawar UTME 2026

  • Hukumar JAMB ta sanar da cewa sakamakon jarabawar UTME 2026 da dalibai suka zana a ranar Alhamis zai fito kafin tsakiyar daren yau Juma'a
  • Hukumar ta bukaci dalibai da su rinka sanya ido a kan shafukan sadarwa na hukumar domin sanin lokacin da sakamakon zai fito a hukumance
  • Fiye da dalibai miliyan biyu ne ake sa ran za su zana wannan jarabawa a fadin kasar nan tsakanin ranar 16 zuwa 22 ga Afrilu, 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta ƙasa (JAMB), ta sanar da lokacin da za a fara fitar da sakamakon jarabawar UTME 2026.

Hukumar JAMB ta bayana cewa za ta fitar da sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2026 da dalibai suka zana a jiya Alhamis kafin tsakiyar daren yau Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama fasinjoji da mugayen makamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

JAMB ta ce za ta saki jarabawar UTME 2026 a daren yau Juma'a
Dalibai na zana jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB). Hoto: @JAMBHQ
Source: Twitter

JAMB: Za a saki sakamakon UTME 2026

Babban mai bada shawara kan sadarwa na hukumar, Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, in ji rahoton Punch.

A cewarsa, ɗaliban da suka zana jarabawar tasu a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, za su iya duba sakamakon su da zaran an kammala tantancewa da dorawa a rumbun adana bayanai na hukumar nan ba da daɗewa ba.

Hukumar ta tabbatar da cewa za a fitar da sanarwa ta musamman a shafukan ta na intanet da zaran an kammala dora sakamakon domin dalibai su iya dubawa.

Sanarwar ta ce:

“Ana sanar da dukkan daliban da suka zana jarabawar UTME 2026 a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu 2026, cewa za a saki sakamakon jarabawarsu a yau, kafin daren ranar ya kare."

Dalibai miliyan 2.2 za su zana JAMB 2026

Wannan mataki na fitar da sakamako cikin sauri na ɗaya daga cikin tsare-tsaren hukumar na inganta aikin ta da kuma rage fargaba a zukatan ɗalibai da iyayen su waɗanda ke jiran sakamakon.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban da suka je yin jarabawar JAMB

An fara zana jarabawar UTME ta bana a duk faɗin ƙasar a ranar Alhamis, inda ake sa ran fiye da ɗalibai miliyan 2.2 ne za su zana jarabawar a cibiyoyin da aka amince da su daga ranar 16 zuwa 22 ga watan Afrilu.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa JAMB ta tsara gudanar da jarabawar UTME a tsarin kashi-kashi a kullum domin rage cinkoso da kuma tabbatar da ingancin tantance ɗalibai.

Gargaɗi ga daliban da za su duba sakamako

Hukumar JAMB ta ba ɗalibai shawara da su rinka bin diddigin kafofin sadarwa na hukumar domin samun sahihan bayanai game da lokacin sakin sakamakon.

JAMB ta gargadi dalibai da su duba sanarwa daga shafukan hukumar kawai.
Shugaban hukumar JAMB, Ishaq Olanrewaju Oloyede da dalibai suna zana jarabawar UTME. Hoto: @JAMBHQ
Source: Twitter

Wannan na da muhimmanci domin guje wa fadawa hannun 'yan damfara ko bin shafukan da ba na hukuma ba waɗanda ke yaɗa labaran ƙarya.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da jarabawar lami-lafiya a sassa daban-daban na ƙasar, inda jami'an hukumar ke sa ido domin tabbatar da cewa ba a tafka maguɗi ko samun matsalolin na'ura da za su kawo cikas ga gudanar da jarabawar ba.

'Yan bindiga sun sace masu zana JMB

A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai a hanyar zuwa zana jarabawar JAMB, lamarin da ya jefa mutane a cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan

Za a samu barkewar cututtuka a Kaduna, Kogi da jihohi 8, gwamnati ta yi bayani

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tabbatar da cewa jami'an rundunar suna cikin daji domin ceto daliban da aka sace a hanyar zuwa zana jarabawar.

Mazauna yankin sun nuna matukar damuwa kan yadda wannan hanyar ta zama matattarar ’yan bindiga masu addabar matafiya da sace dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com