JAMB
Hukumar JAMB ta ce sam bata tilastawa dalibai sai sun cire hijabi ba wajen rubuta jarrabawar JAMB, ta yi karin haske kan abin da take nufi da bayanai kan hijabi.
JAMB za ta fara sayar da fom din jarabwar UTME 2026; yayin da kuɗin rajista ya kai ₦7,200, kuma an sanya ranar 16 ga Afrilu, 2026 domin fara jarrabawar ga ɗalibai.
Hukumar JAMB ta saki cikakken bayani da hanyoyin da dalibai za su bi domin yin rajistar UTME 2026, tare da gargaɗi kan bayanan NIN, matsalolin shigar da bayanai.s
Gwamnatin Tarayya ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa JAMB ba zai sake zama wajibi wajen samun gurbin shiga jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandire.
Hukumar NUC ta yi gargadi ga dalibai yayin da ta fitar da sunayen jami’o’in bogi 58 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a fadin Najeriya, suna ba da digiri marasa inganci.
JAMB ta sanar da cewa Okeke Chinedu ne ya fi maki kowanne dalibi samun maki a jarabawar UTME 2025, amma an gano sabani kan shigarsa jami'ar Nsukka a baya.
Ministan ilimi ya, Tunji Alausa ya ce za a fara dakatar da duk wani dalibi da aka samu da satar amsa tsaron shekaru uku ba tare da rubuta NECO, WAEC ko JAMB ba.
Yan Najeriya sun nuna takaici kan yadda ɗalibai suka faɗi jarabawar share fagen shiga jami'o'i da sauran manyan makarantu watau UTME, sun tattaro dalilai.
JAMB ta ce ɗalibai 379,997 daga jihohi 6 za su sake rubuta UTME bayan kuskure a sakamakon jarabawar, yayin da WAEC ta amince za ta taimaka a sake jarabawar.
JAMB
Samu kari