Muhimman Dalilai 3 da Suka Taimaka Wajen Faɗuwar Ɗalibai Jarabawar JAMB 2025

Muhimman Dalilai 3 da Suka Taimaka Wajen Faɗuwar Ɗalibai Jarabawar JAMB 2025

FCT Abuja - A ranar Juma'a 9 ga watan Mayu, 2025, Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu a Najeriya (JAMB) ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME 2025.

Ɗalibai daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun zana jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da sakandire watau UTME ta bana a watan Afrilu zuwa Mayu, 2025.

Hukumar JAMB.
Wasu daga cikin dalilan da suka jawo faɗuwar yara jarabawar JAMB 2025 Hoto: JAMB
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa ɗalibai sama da miliyan 1.9 ne suka yi rijista kuma suka zauna jarabawar UTME a cibiyoyin CBT daban-daban a ƙasar nan.

JAMB dai ta mayar da rubuta jarabawar UTME ta na'ura mai kwakwalwa, ma'ana gaba ɗaya an daina amfani da biro da takarda sai dai kwamfuta.

JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME

A makon jiya, hukumar JAMB ta saki sakamakon jarabawar 2025 a ranar Juma'a da ta gabata, inda ta ce sama da kaso 75% sun ci maki ƙasa da 200.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Bussines Day ya nuna cewa wannan ne karo na uku aka samu faɗuwa jarabawar UTME mafi muni a Najeriya tun 2016.

Kusan kashi 79% na daliban da suka rubuta jarrabawar sun samu kasa da maki 200 daga cikin maki 400 da ake bukata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce da damuwa a fadin kasar.

Abubuwan da suka jawo aka fadi jarrabawar JAMB

Wannan rahoto na musamman ya bibiyi wasu daga cikin muhimman dalilan da suka haddasa wannan gagarumar faduwa:

1. Matsalar na’ura da tsarin fasaha

Yayin da ake ta surutu kan gagarumar faɗuwa a UTME ta bana, shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya fito ya amsa cewa an samu kura-kurai.

A taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Laraba, Farfesa Ishaq Oloyede, ya nemi afuwar iyaye kan abin da ya jawo rashin nasarar 'ya 'yansu.

Kura-kuran da aka samu sun shafi kwamfutoci da tsarin gudanar da jarrabawar a cibiyoyi da dama, lamarin da ya jawo faɗuwar dubannin ɗaruruwan ɗalibai.

Wurin zana JAMB.
Ana samun waɗanda ba su iya danna kwamfuta ba a JAMB Hoto: Getty Image
Asali: UGC

Hukumar JAMB ta amsa cewa wasu daga cikin cibiyoyin CBT 157 sun yi jarrabawar ba tare da an sabunta wasu muhimman bayanai da manhajoji ba.

Wannan matsala ta shafi fiye da dalibai 370,000 inda aka samu jarrabawar da ke da tambayoyi marasa amsa, tangarɗa wajen fitar da sakamako da kuma tsayawar na’ura.

Wannan ya tilastawa Hukumar JAMB ta shirya sake jarrabawa daga 16 zuwa 19 ga watan Mayu, 2025.

2. Rashin isasshen shiri da ilimin kwamfuta

Baya ga matsalolin fasaha da aka samu a jarabawar UTME 2025, rashin isasshen shiri daga bangaren dalibai ya taka muhimmiyar rawa.

Haka zalika wasu daga cikin ɗalibai musamman waɗanda suka fito daga karkara da ƴaƴan masu ƙaramin ƙarfi ba su iya amfani da kwamfuta ba.

A wani rahoton da Leadership ta tattaro, an gano cewa akwai ɗalibai da dama da ke zuwa jarabawa a cibiyoyin ba tare da ilimin amfani da na'ura mai kwakwalwa ba.

Rahoton wani mai sa ido ya bayyana cewa wasu daga cikin ɗalibai ba su san yadda ake amfani da madannan kwamfuta ba, balle su iya sarrafa ta har su yi jarabawa a ciki.

3. Katsewar wuta da ɗaukewar na’ura

Wanna matsala da aka fiye samu ta ɗaukewar wutar lantarki, ko kwamfuta na ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo faɗuwa lr da ake samu a jarabawar UTME.

Dalibai da dama sun fuskanci ƙalubalen katsewar wutar lantarki wanda ke jawo tsayawar jarabawa a cibiyoyin CBT har sai masu kula da wurin sun shawo kan lamarin.

Wani mai kula da masu zana jarabawar ya ce ɗalibai da dama kan ruɗe wajen sake shiga idan an dawo da wuta, wasu kuma su danna madannin kammalawa.

Rahotanni sun nuna cewa wannan matsala na taka raya wajen rashin nasarar ɗalibai da dama, kuma ya kamata hukumar JAMB ta daƙile faruwar irin haka.

Majalisa za ta binciki kuskuren da JAMB ta yi

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilan Tarayya ta amince za ta gudanar da bincike kan yadda aka samu tangarɗa wurin fitar da sakamakon UTME 2025.

Majalisar ta cimma matsaya ne a zamanta na ranar Alhamis, bayan ta amince da wani kudurin gaggawa da dan majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo, ya gabatar.

Daga ƙarshe, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gina cibiyoyin CBT a kowanne karamar hukuma (LGA) a fadin ƙasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262