"Yara na 3 Sun Mutu," Magidanci Ya Sabawa Bayanin Sojoji kan Kuskuren Jefa Bam a Neja
- Mazauna kauyen Guradnayi da ke kusa da Kusasu a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun tabbatar da cewa sojoji sun jefa masu bam
- Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojin Najeriya ta musanta kuskuren kashe fararen hula a harin da ta kai kauyen, ta ce yan bindiga kadai ta kashe
- Wani magidanci da ke kwance yana jinya, Victor Solomon ya ce yaransa uku sun mutu sakamakon bam din da sojojin suka saki a kauyen
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Wani magidanci, Victor Solomon mai shekaru 50 ya bayyana cewa ya rasa ‘ya’yansa uku sakamakon harin bama-bamai da sojoji suka kai bisa kuskure a jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne kauyen Guradnayi da ke kusa da Kusasu a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu

Source: Original
Ana zargin sojoji sun kashe mutanen gari
Ana zargin akalla mutane 13 ne, mafi yawansu yara, suka mutu sakamakon harin saman da aka kai kauyen da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, kamar yadda Premium Times ta kawo.
Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi da ta gabata yayin da jiragen yaki ke bin diddigin wasu ‘yan bindiga da ke kan babura a yankin.
Mutane sun bayyana abin da ya faru
Victor Solomon, wanda yake kwance a gadon asibiti yana jinya, ya ce yana barci ne misalin karfe 5:00 na safe lokacin da harin ya afku, lamarin da ya jikkata fuskarsa sosai.
“Ban san ko zan rayu ba. Na samu munanan raunuka a fuska kuma ina cikin matsanancin ciwo. Muna bukatar taimakon gwamnati," in ji shi.
Shi ma Gideon Bamaiyi ya shaida wa Daily Trust cewa tun da farko ‘yan bindiga sun bi ta yankin kamar yadda suka saba kafin sojoji su jefa masu bam din.
Ya ce mutane 13 ne suka mutu, ciki har da yara bakwai da suke gudun hijira gidan yayansa lokacin da bam din ya sauka.
Halin da mutane ke ciki bayan harin
A cewarsa, wasu mutum shida suna karbar magani a wani asibiti mai zaman kansa da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro.
Ya kara da cewa har zuwa yammacin Lahadi, mutum biyar daga cikin wadanda suka jikkata, ciki har da wata karamar yarinya, suna cikin mawuyacin hali ba tare da sun farfado ba.

Source: Facebook
Bamaiyi ya ce asibitin ya bukaci a biya N400,000 domin yi wa daya daga cikin matan da suka jikkata tiyata, yana mai kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka.
Wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar harin saman, amma bai yi karin bayani kan yawan fararen hular da suka mutu ba.
Sojoji sun musanta kashe fararen hula a Neja
Tun farko, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton cewa fararen hula sun mutu a hare-haren sama da aka kai a jihar Neja.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Ayyukan Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, ya ce farmakin ya auna ne kan sansanonin ‘yan bindiga kaɗai.
Onoja ya ce bayanan da aka samu daga majiyoyin sirri sun tabbatar da cewa hare-haren sun yi daidai da wuraren da aka nufa musamman a Kusasu, Katerma da Bokko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
