Rundunar Sojin Sama Ta Fayyace Abin da Ya Faru a Neja, Ta Karyata Zargin Kashe Mutanen Gari

Rundunar Sojin Sama Ta Fayyace Abin da Ya Faru a Neja, Ta Karyata Zargin Kashe Mutanen Gari

  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton cewa fararen hula sun mutu a hare-haren sama da aka kai a jihar Neja a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2026
  • Hedikwatar tsaro ta ce hare-haren sun hallaka yan bindiga masu tarin yawa da suka fara taru wa domin kai wa mutanen da ba ruwansu munanan hare-hare
  • Sojoji sun bayyana cewa an gudanar da farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan taruwar ‘yan ta’adda, sannan aka bi sawunsu har zuwa yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe fararen hula a hare-haren sama da sojoji suka kai a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Ayyukan Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar ranar Lahadi, ya ce farmakin ya auna ne kan sansanonin ‘yan bindiga kaɗai.

Kara karanta wannan

Masu neman takara 6 sun hakura, an bar wa Shekarau tikitin sanatan Kano ta Tsakiya

Rundunar sojin sama ta ce jami'anta ba su kashe fararen hula ba
Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke a lokacin da ya je Majalisar dattawa Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu bayanan sirri a ranar 9 ga Mayu, 2026 cewa manyan ‘yan bindiga sun taru a ƙauyen Lukupe da ke Shiroro.

Sojoji sun musanta kashe fararen hula

Business day ta kawo labarin cewa bayan samun bayanai, rundunar UAV ta sojojin ta kai jerin hare-haren sama tsakanin 11.59 na dare zuwa ƙarfe 6.00 na safe a wasu wuraren da ake zargin mafakar ‘yan bindiga ne.

Ƙauyukan da aka kai wa harin sun haɗa da Katerma, Bokko, Kusasu da Kuduru, duk a ƙaramar hukumar Shiroro.

Onoja ya ce bayanan da aka samu daga majiyoyin sirri sun tabbatar da cewa hare-haren sun yi daidai da wuraren da aka nufa musamman a Kusasu, Katerma da Bokko.

Ana zargin sojojin sama sun kai hari bisa kuskure kan fararen hula a Neja
Taswirar jihar Neja inda ake zargin sojojin sama da barin wuta kan jama'a Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“A wani ɓangare na aikin rundunar sojin Najeriya na kawar da duk wani nau’in rashin tsaro a ƙasar nan, bayanan sirri sun nuna taruwar ‘yan bindiga a Lukupe da ke Shiroro.”

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari

Ya ƙara da cewa:

“Daga nan ne rundunar UAV ta sojojin ta kai hare-haren sama a wuraren da ‘yan bindiga suke a Katerma, Bokko, Kusasu da Kuduru. Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai farmakin daidai wuraren da aka sa a gaba.”

Sojoji sun ce an kashe ‘yan bindiga 70

A cewar sanarwar, kimanin ‘yan bindiga 70 ne suka mutu a Kusasu kaɗai sakamakon harin saman. Onoja ya ce an ga waɗanda suka tsira suna kwashe gawarwakin abokanansu domin yi musu jana’iza.

Hedikwatar tsaron ta kuma bayyana cewa an hangi sama da ‘yan bindiga 200 ɗauke da makamai a kan babura suna tafiya zuwa Zango domin sake haɗuwa.

Sanarwar ta ce wasu ‘yan bindigar daga Bokko su ma suna kan hanyar zuwa yankin, inda ake zargin suna shirin kai hari Sarkin Pawa, Kuchi ko cibiyoyin jami’an tsaro na gwamnati.

Haka kuma, sojojin sun ce an gano wata ƙungiyar ‘yan bindiga na taruwa a Kopa da ke gabashin Mongoro, lamarin da ya nuna yiwuwar barazana ga jami’an tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Ana fargabar sabon harin sojoji ya kashe mutanen gari a jihar Neja

Sai dai duk da rahotannin da ke yawo cewa fararen hula sun mutu, Hedikwatar Tsaro ta nace cewa an gudanar da aikin ne bisa sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da kasancewar ‘yan ta’adda a wuraren da aka kai hari.

Ana tsoron harin sojoji ya kashe jama'a

A baya, kun samu labarin cewa jama'a sun shiga fargaba bayan zargin wasu dakarun sojojin saman Najeriya sun bi 'yan ta'adda zuwa kauyen Guradnayi da ke jihar Neja tare da kai masu hari.

Amma ana tsoron an hallaka fararen hula 'yan ba ruwana da dama a sabon harin sama da aka kai a ƙauyen a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2026 inda ake tantama an adadin da suka mutu.

Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne yayin da jirgin soji ke bin ‘yan ta’adda da suka ratsa yankin, kuma 'yan bindigan sun ci gaba da ta'addancinsu duk da harin tare da sace tumakin jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng