Majalisa: Tirka Tirkar da Ta Jawo Zazzafan Musayar Yawu tsakanin Oshiomole da Akpabio
- Rikici ya ɓarke a Majalisar Dattawa tsakanin Godswill Akpabio da Adams Oshiomhole kan sababbin dokokin shugabancin majalisa
- Sabuwar dokar ta hana sababbin sanatoci da waɗanda ba su yi wa’adi biyu a jere ba neman manyan kujeru a majalisar
- Masana sun ce sauyin dokar na iya zama wata dabara ta siyasa domin hana wasu sanatoci samun damar shugabanci a majalisa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sababbin bayanai sun bayyana kan musayar yawu da aka samu tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole kan gyaran dokokin majalisar.
Sababbin dokokin da aka amince da su sun ƙara tsaurara sharudan neman kujerun shugabanci a Majalisar Dattawa ta 11 da ake sa ran za a kafa a watan Yunin 2027.

Kara karanta wannan
Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki

Source: Facebook
The Guardian ta wallafa cewa dokar ta hana sanatocin da suka shiga majalisa karo na farko ko waɗanda ba su yi wa’adi biyu a jere a majalisun tara da ta 10 ba damar neman kujerun shugaban majalisa ko mataimakinsa.
An yi sababbin dokoki a Majalisar dattawa
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan mataki zai shafi gwamnoni masu wa’adi na biyu da ke shirin zuwa majalisar dattawa a 2027, daga ciki har da gwamnonin Gombe, Yobe, Nasarawa, Bauchi, Ogun da Kwara.
Haka kuma wasu tsofaffin sanatoci da ke son dawowa majalisa za su iya fuskantar matsala saboda sabon tsarin.
Majalisar dattawa ta yi gyaran dokar ne bayan zaman sirri da ta gudanar ranar Talata, 5 ga watan Mayu na shekarar 2026.
A sabon sashe na huɗu na dokar, an bayyana cewa za a yi la’akari da matsayi da ƙwarewar sanatoci wajen zaɓen shugabannin majalisa.
Sauyin da aka yi a dokar majalisa

Kara karanta wannan
Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci
An kuma ƙara wani sashe da ya ce duk sanatan da bai yi wa’adi biyu a jere ba ba zai iya neman manyan kujerun majalisa ba.
Rahotanni sun nuna cewa Oshiomhole bai gamsu da wannan sabon sharadi ba saboda yana ganin an tsara shi ne domin hana shi da wasu masu neman shugabanci.
Rikicin ya fara ne lokacin da Akpabio ke karanta bayanan zaman ranar Talata a zaman majalisar na ranar Laraba 6 ga watan Mayu na 2026.
Lokacin da aka kai ga saaaan da suka shafi sababbin dokokin shugabanci, Oshiomhole ya riƙa ɗaga neman a ba shi izinin magana domin dakatar da amincewa da su.

Source: Facebook
Sai dai Akpabio ya yi watsi da ƙoƙarin nasa tare da tunatar da sanatoci cewa akwai takamaiman matakai da ake bi kafin ɗaga irin wannan batu.
Ko bayan bayanin da wasu sanatoci suka yi, Oshiomhole ya ci gaba da ƙoƙarin yin magana, abin da ya fusata Godswill Akpabio.
Farfesa Murtala Muhammad na Jami’ar North West da ke Kano ya ce abin da ya faru ya nuna raunin tsarin dimokuraɗiyya da yadda ake amfani da dokoki wajen fifita wasu ɓangarori.
Shi ma shugaban Ƙungiyar Masana Kimiyyar Siyasa ta Najeriya, Farfesa Hassan Saliu, ya ce duk da cewa irin wannan tsari ba sabon abu ba ne, lokaci da yanayin da aka kawo dokar sun jawo zarge-zargen cewa ana son hana wasu masu burin shugabanci damar takara.
Rikici ya ƙare tsakanin Akpabio da Oshiomole
A baya, mun wallafa cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi musayar yawu mai zafi da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole.
Lamarin ya faru ne lokacin da Akpabio ke karanto bayanan zaman Majalisa na ranar Talata, 5 ga watan Mayu na shekarar 2026 wanda sanatoci suka gyara dokar neman shugabanci.
Sanata Adams Oshimhole ya yi kokarin yin magana amma shugaban Majalisar ya hana shi, lamarin da ya jawo musayar yawu na akalla mintuna 15 a zaman da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
