Yadda wasu Jaruman Kannywood suka yi auren mutu'a

Yadda wasu Jaruman Kannywood suka yi auren mutu'a

Wani sabon rudani ya yi wa masana'antar Kannywood mai kula da shirin fina-finan Hausa dabaibayi, inda aka samu jarumi kuma mai shirya fina-finai, Isa I. Isa da kuma jaruma Sadiya Haruna da tona wa junansu asiri.

Isa I. Isa da Sadiya Haruna
Isa I. Isa da Sadiya Haruna
Asali: Instagram

Kamar yadda kafar watsa labarai ta freedomradionig.com ta wassafa a shafinta, ta ce wannan rudani ya samo asali ne tun yayin zargin da jaruma Sadiya ta yi a kan jarumi Isa. Jarumar dai ta yi zargin ne gabanin ta kama sunansa inda kuma daga bisani ta bayyana sunansa karara.

Cikin wani faifan bidiyo da jarumar ta saki na kalubalantar jarumin da ya fito ya kare kansa, ta zarge shi da cewa sunyi auren mutu'a, wato dai auren biyan bukata tare da daukewa juna sha'awa na wani tsawon lokaci kayyadadde.

Hakazalika shi ma jarumin ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na zauren sada zumunta, inda labartawa duniya cewa ya aikata wasu ababe na rashin kyautawa da kuma rashin daidai tare da neman gafarar al'umma da masoyansa.

Freedom Radio Nigeria ta tattaro cewa, jarumin daga bisani ya goge wannan bidiyo, amma dai tuni aikin gama ya gama domin kuwa fasahar zamani ta sanya bidiyon ya yi duk wani shawagi da zai yi a dandalin YouTube.

KARANTA KUMA: EFCC ta mallakawa gwamna AbdulRazaq N111.4m da ta kwato a hannun barayin gwamnatin jihar Kwara

A wani lokaci da ya gabace mu, jarumi Isa I. Isa cikin wani bidiyo yayin amsa tambayar menene ainihin alakarsa da jaruma Sadiya Haruna, ya ce ba komai bane face ta kasance matarsa.

Sa'o'i uku bayan faruwan hakan, ita ma kuma jaruma Sadiya ta wallafa wani sako a shafinta na Instagram da cewa Isa ya taba debo mata 'yan sanda har gida.

Daya daga cikin jaruman dandalin Kannywood wadda ita ma ta yi kaurin suna a zaurukan sada zumunta, Muneerat Abdussalam, ta bayyana mamakin yadda rikici ya barke a tsakanin jaruman biyu, inda ta bayyana Isa da kuma Sadiya a matsayin masoya biyu da suka taba kai mata ziyara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel