Tirkashi wani aikin sai gwari: Wasu mata sunyi musayar mazajensu domin samun farin cikin junansu

Tirkashi wani aikin sai gwari: Wasu mata sunyi musayar mazajensu domin samun farin cikin junansu

- Wasu mata guda biyu a garin Busia dake kasar Kenya sunyi musayar mazajen su

- Lamarin ya biyo bayan wani abu da ya faru, inda mijin daya yaje ya karo aure ashe matar da ya auro da mijinta

- Hakan ya sa tsohuwar matarsa zuwa ta auri mijin waccan matar da ya auro

Lilian Weta mai shekaru 28, wacce ke da 'ya'ya guda uku, da kuma Millicent Auma mai shekaru 29 mai yara guda biyu, sun bazu a shafukan sada zumunta na zamani, bayan an gano yadda matayen guda biyu suka yi musayar mazajensu domin su samu farin ciki.

Hakan ya faru bayan mijin Lilian wanda aka bayyana sunan shi da Kevin ya auri Millicent a matsayin matar shi ta biyu, ashe ita kuma tana da mijinta mai suna Christopher Abwire wanda ta gudu ta bari.

Rashin jin dadin abinda mijinta yayi mata na karo mata kishiya, Lilian ta yanke shawarar zuwa wajen Christoper, tsohon mijin Millicent, inda ta rarrashi akan ya aureta kuma ya amince da bukatar ta.

KU KARANTA: Allah wadan naka ya lalace: An kama Malamin Addini da yake sanya mabiyansa mata suyi tsirara ya dinga daukar su hoto

A cewar Christoper wanda yayi magana da manema labarai a gidan shi, kawai ya nemi matarsa Millicent ya rasa ne, sai daga baya yake samun labarin ta yi aure a wani waje.

Legit.ng ta gano cewa ma'auratan sun hadu a karshe bayan daya daga cikin matan ta taso da maganar musayar. Sai dai kuma bayan sun hadu dukan su sun yarda akan su cigaba da zama a yadda suke.

Sabon mijin Millicen ya bayyana cewa bayan sun yi musayar yanzu yana jin dadi fiye da wancan lokacin, domin yanzu sabuwar matarshi tana sanya shi farin ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel