Tirkashi: Bidiyo Ya Nuna Yadda Wasu Makwabta Suka Yi Musanyan Matansu da 'Ya'yansu, Sun Fadi Dalili

Tirkashi: Bidiyo Ya Nuna Yadda Wasu Makwabta Suka Yi Musanyan Matansu da 'Ya'yansu, Sun Fadi Dalili

  • Wasu makwabta guda biyu sun ba da mamaki yayin suka yi musanyan matansu da ‘ya’yansu ga juna
  • Badakalar ta fara ne yayin da makwabtan suke zuwa gidan junansu ziyara kafin daga baya ya koma soyayya
  • Bayan sanin abin da ke faruwa, sai makwabtan suka yanke shawarar kawo karshen matsalarsu ba tare da fada ba

Wasu mazaje guda biyu makwabta sun yi musayar matansu da ‘ya’yansu a wani biki da ya bai wa mutane mamaki.

Kafar Afrimax da ta wallafa faifan bidiyon, ta bayyana cewa wadanda suka yi musayar matan nasu makwabta na kut-da-kut.

Ma'aurata
“Sun Fara Son Junansu”, Wasu Makwabta Sun Yi Musanyan Matansu a Wani Faifan Bidiyo. Hoto: Afrimax.
Asali: Youtube

Afrimax ta bayyana cewa Lilian ta auri Kelvin yayin da Immaculate ta auri Christopher.

A matsayinsu na makwabta suna kai ziyara ga junansu kafin ziyarar ta rikide ta koma soyayya tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makwabtan sun yanke hukuncin musanyan ne don kaucewa rikici

Makwabatan sun ci gaba da mu’amala a boye da kuma zuwa gidajen juna har zuwa lokacin da sirrin ya bayyana.

Ma’auratan sai suka yanke hukuncin gyara matsalar ta hanyar musanyan matansu da kuma bikin aure a tsakaninsu don tabbatarwa.

Daga cikin yarjejeniyar akwai yin musanyan ‘ya’yansu gaba daya da matan.

Faifan bidiyon ya jawo kace-nace a kafar sada zumunta ta zamani. Kalli bidiyon:

Martanin jama'a a kafar YouTube

Mutane da dama masu ta'ammali da kafar sada zumunta sun yi martani:

LOX.4:

“Kuyi hakuri, amma wannan dai ba kyau.”

Chansa Jonathan:

“Wasa suke yi ne, wani irin wasa ne wannan, za a iya musanya mata? A’a.”

Cher 007:

“Dokar Allah ita ce kadai doka.”

Amundam Marline:

“Mun gode da wannan izina, jan kati.”

SassySelkie72:

“Ya kamata muna bin dokokin Allah, da farko dai ba kullum ne ake bin dokokin al’umma ba.”

Sophia Cherrington:

“Za su kone a wuta idan suka ci gaba da wannan wautar, da wasa da aure, Allah ne ya saka dokokin aure ba mu ba.”

Ba Kasuwa: Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Shago Bayan Shafe Makwanni 3 Babu Ciniki

A wani labarin, wani faifan bidiyo ya yadu inda aka gano wata budurwa ta na kwalla saboda rashin ciniki a shago.

An gano budurwar ta na zagawa a shagon ta na hawaye da cewa makwanni uku kenan babu wanda ya zo ya sayi ko abin kwabo daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel