Shugaban Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, IGP Disu Ya Tsoma Baki kan Zargin Kisan Dadiyata
- Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta fara gudanar da bincike kan zargin wasu jami'anta da kashe 'dan gwagwarmaya, Abubakar Idris Dadiyata
- Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu ne ya ba da umarnin gudanar da binciken bayan korafe-korafen jama'a
- An ruwaito cewa lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama daga Kano, Abba Hikima, ya miƙa koragi ga rundunar 'yan sanda
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya karbi korafe-korafen da aka shigar kan zargin kisan 'dan gwagwarmaya a kafafen safa zumunta, Abubakar Idris Dadiyata.
Shugaban yan sandan ya umarci sashen sa ido na rundunar ‘yan sanda ya binciki zargin da ake yi wa jami’ai biyu dangane da ɓatan malamin jami’a kuma ɗan gwagwarmaya, Dadiyata.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro cewa Jami’an da ake zargi sun haɗa da CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba.
Abba Hikima ya kai kokr ga IGP
Umarnin binciken ya biyo bayan wasu koke-koke da lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama daga Kano, Abba Hikima, ya miƙa wa rundunar ‘yan sanda a ranar Juma’a.
Takardun korafe-korafen sun yi ishara da wasu kalamai da Muhammad Musa Kamarawa, tsohon hadimi ga tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi.
Kamarawa ya yi zargin cewa jami’an sun yi masa barazana, inda suka yi ikirarin kashe Dadiyata da wasu mutane a gabansa a wani wuri da ake kira Operations Yaki a Kaduna.
A cikin ɗaya daga cikin koken, Abba Hikkma ya bayyana cewa idan zargin ba gaskiya ba ne, cikakken bincike zai wanke jami’an daga zargi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
An buƙaci bincike mai zaman kansa
Takardun koken sun nuna damuwar jama’a kan ɓatan Dadiyata tare da kira da a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar lamarin.
Da yake martani, Sufeto Janar na ‘yan sanda ta bakin babban jami’in ofishinsa, CF Lateef Adio Ahmed, ya ce an tura batun zuwa ga mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashen sa ido domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya
Har ila yau, rundunar ta tabbatar wa masu koken cewa tana da ƙudurin tabbatar da adalci da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da laifi.

Source: Facebook
Har yanzu ba a gano Dadiyata ba
An sace Dadiyata, malamin jami’a kuma ɗan gwagwarmaya a kafafen sada zumunta, daga gidansa da ke Barnawa a Kaduna a watan Agustan 2019.
Tun daga lokacin, lamarin ya kasance ɗaya daga cikin manyan shari’o’in da har yanzu ba a warware ba a Najeriya, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen neman gaskiya da adalci daga jama’a.
El-Rufai ya yi magana kan batan Dadiyata
A wani labarin, kun ji cewa tsohon hwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya musanta hannun gwamnatinsa a batun batan Abubakar Idris, watau Dadiyata.
Nasir El-Rufai ya nace cewa dukkan zarge-zarge da ke alaƙanta gwamnatinsa da dauke wannan matashi kuskure ne kuma ba su da kamshin gaskiya.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Dadiyata, wanda ɗan asalin jihar Kano ne, ya fi mayar da hankali ne wajen sukar Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kawai.
Asali: Legit.ng
