'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Ci Karo da Sojoji da Yan Sanda a Jihar Kano

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Ci Karo da Sojoji da Yan Sanda a Jihar Kano

  • Yan bindiga sun shiga yankin karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, sun kashe mutum daya tare da sace shanu sama da 300
  • Kansilan mazabar Mainika, Auwal Abdussalam Barau ya ce sojoji da yan bijilanti sun kwato kusan shanu 100 daga hannun maharan
  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukiwar lamarin, ta ce dakarunta da yan JTF sun fatattaki 'yan bindigar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - ‘Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mainika da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano, inda suka kashe wani makiyayi tare da sace shanu sama da 300.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, 2026.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ce da yake tabbatar da faruwar lamarin, kansilan Mainika, Auwal Abdussalam Barau, ya ce maharan sun zo ɗauke da mugayen makamai, kuma ana zargin sun shigo ne daga jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda ƴan bindiga suka kashe masu juna 2 da tarin mutane a Filato

“Sun zo wajen ƙarfe 6:00 na yamma ranar Laraba suka yi awon gaba da shanu sama da 300 tare da kashe wani bafullatani makiyayi da ya yi ƙoƙarin hana su," in ji shi.

An ceto wasu daga cikin shanun

Kansilan ya ce bayan harin, dakarun sojoji da ‘yan sintiri sun hada tawaga domin bin sawun maharan.

Auwal Barau ya ce:

"Bayan sun fafata, dakarun sun yi nasarar dawo da sama da shanu 100. A baya yan bindiga sun sace wata matar aure da wani matashi, daga baya kuma suka dawo suka sace wani dattijo. Wannan shi ne hari na uku da suka kai mana.”

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun tabbatar musu da cewa za a ci gaba da ƙoƙarin ƙwato sauran shanun da aka sace, cewar rahoton Leadership.

An nemi kafa sansanin soja

Auwal Barau ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta duba yiwuwar kafa sansanin soja a yankin domin dakile hare-haren da ake kai wa al’ummar yankin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kuma tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta tare da haɗin gwiwar rundunar JTF sun samu nasarar ƙwato shanu 67, jaki guda da tunkiya guda daga hannun barayin.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya

Yan sanda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Wane mataki yan sanda suka dauka?

Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu rahoto a ranar 6 ga watan Mayu, 2026 da misalin ƙarfe 6:15 na yamma cewa wasu da ake zargin barayin shanu ne sun kai hari wasu ƙauyuka a Gwarzo da kewaye.

Ya ce:

“Jami'an ‘yan sanda da hadin gwiwar dakarun JTF sun kai dauki gafin, kuma da maharan suka hango su sai suka buɗe musu wuta.
"Dakarun tsaro sun yi artabu da su, amma sun fi ƙarfinsu saboda suna da dabaru da kwarewa, lamarin da ya tilasta musu barin dabbobin tare da tserewa.”

Yan bindiga sun shiga Rogo a Kano

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano.

Maharan sun kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya sa aka kara tsaurara matakan tsaro a yankin.

Kwamandan kungiyar ‘yan sa-kai ta Rogo, Alhaji Haruna Barhaya, ya tabbatar da aukuwar harin yayin da yake yi wa hukumomin yankin bayani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262