Mutuwa Ta Ratsa Iyalan Tsohuwar Ministar Buhari, Ta Yi Babban Rashi

Mutuwa Ta Ratsa Iyalan Tsohuwar Ministar Buhari, Ta Yi Babban Rashi

  • Anthony Adeosun, mijin tsohuwar Ministar Kudi, Kemi Adeosun, ya rasu yana da shekara 62 a duniya
  • Iyalan marigayi Anthony Adeosun sun sanar da cewa ya rasu a Legas ranar Laraba, 5 ga watan Agustan shekarar 026
  • Marigayin ya mutu ya bar matarsa Kemi Adeosun, 'ya'yansa da kuma 'yan uwansa, ciki har da Adewale Adeosun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas – Anthony Adeniyi (Niyi) Adeosun, mijin tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun, ya rasu yana da shekara 62.

Iyalan Anthony Adeosun sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka ce ya rasu a ranar Laraba, 5 ga watan Agusta, 2026, a jihar Legas.

Kemi Adeosun ta rasa miji
Tsohuwar ministar Kudi, Kemi Adeosun Hoto: Kemi Adeosun
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton rasuwar marigayin a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan shekarar 2026.

Sanarwar mai taken "Sanarwar rasuwar Mista Anthony Adeniyi (Niyi) Adeosun", wadda Fasto C. A. Adeosun ya fitar a madadin iyalan, ta tabbatar da rasuwar marigayin.

Kara karanta wannan

Siyasar Amurka: Abdul El Sayed ya gaza hakuri, ya yi wa Trump zazzafan martani

Iyali sun bayyana halayen Anthony Adeosun

A cewar sanarwar da iyalan suka fitar, Anthony Adeosun fitaccen ɗan kasuwa ne kuma Kirista mai sadaukar da kai, wanda ya yi tasiri mai kyau ga rayuwar duk wanda ya san shi, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Sanarwar ta ce:

"Cikin baƙin ciki mai girma, amma tare da miƙa kai ga nufin Allah Maɗaukakin Sarki, iyalan Adeosun suna sanar da rasuwar ƙaunataccen mijinmu, mahaifinmu kuma ɗan'uwanmu, Mista Anthony Adeniyi (Niyi) Adeosun, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa ranar Laraba, 5 ga watan Agusta, 2026, a Legas."
"Ya rasu yana da shekara 62. Niyi fitaccen ɗan kasuwa ne kuma Kirista mai tsananin biyayya, wanda gaskiyarsa, karamcinsa da ƙaƙƙarfan imaninsa suka taɓa rayuwar duk wanda ya san shi."
"Ya rayu cikin ƙwazo, bautar Allah da kuma sadaukar da kai ga iyalansa da al'ummarsa."

Iyalan sun nemi addu'a

Iyalan marigayi sun kuma bayyana cewa za a sanar da jama'a bayanan jana'iza da shirye-shiryen binne marigayin bisa tsarin addinin Kirista nan gaba kadan.

Kara karanta wannan

An yi rashin babban malamin Musulunci a Maiduguri, Sheikh Dazigau Tijjani

Anthony Adeosun ya rasu ya bar matarsa, Kemi Adeosun; 'ya'yansa; da kuma 'yan uwansa, ciki har da wanda ya kafa Kuramo Capital, Adewale Adeosun.

A ƙarshen sanarwar, iyalan sun bayyana cewa:

"Muna godiya ga duk wanda ya aiko da addu'o'i, ta'aziyya da goyon baya. Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba shi hutu na har abada."
Mijin Kemi Adeosun ya rasu
Marigayi Anthony Adeosun, miji ga Kemi Adeosun Hoto: @HMKemiAdeosun
Source: Twitter

Mawakin siyasa a Kano ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawakin siyasa na Kano, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, ya rasu a ranar Lahadi, 2 ga Agustan 2026, a wani asibiti da ke jihar Kano.

Rasuwar mawakin ta jefa iyalansa, 'yan'uwansa, abokansa, masoya da sauran al'umma cikin alhini, musamman waɗanda suka san shi da kuma waɗanda suka kasance suna bibiyar ayyukansa a fagen waƙa.

Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mawakan siyasa a Arewacin Najeriya, inda waƙoƙinsa suka samu karɓuwa sosai a tsakanin masoya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng