Siyasar Amurka: Abdul El Sayed Ya Gaza Hakuri, Ya Yi wa Trump Zazzafan Martani

Siyasar Amurka: Abdul El Sayed Ya Gaza Hakuri, Ya Yi wa Trump Zazzafan Martani

  • Ɗan takarar Sanatan jam'iyyar Democrat a Michigan, Abdul El-Sayed, ya yi watsi da kalaman suka da Donald Trump ya yi masa
  • El-Sayed ya ce abin da ya fi damun al'ummar Michigan shi ne tsadar rayuwa, ba zagin siyasa ba yayin da ya fara yakin neman zaɓe
  • Ya kuma yi alƙawarin rage tsadar rayuwa, faɗaɗa ayyukan kiwon lafiya da magance matsalar gidaje idan aka zaɓe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Michigan, Amurka – Ɗan takarar Sanatan jam'iyyar Democrat a jihar Michigan, Abdul El-Sayed, ya yi watsi da kalaman suka da shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa bayan nasararsa a zaɓen fitar da gwani.

El-Sayed ya bayyana cewa maimakon yin zage-zage, ya kamata Trump ya mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi tsadar rayuwar al'ummar Amurka.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Shugaba Trump ya yi magana kan batun karancin makaman Amurka

Donald Trump da Abdul El-Sayed
Donald Trump a gefen hagu da Abdul El-Sayed a gefen dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Anadolu ta rahoto cewa El-Sayed ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar Democrat gabanin babban zaɓen watan Nuwamba.

Martanin El-Sayed ga Trump

Trump ya yi wa El-Sayed lakabi da "mai ra'ayin gurguzu" da kuma wasu kalamai masu zafi bayan kammala zaɓen fidda gwani.

Yeni Safak ta wallafa cewa El-Sayed ya ce:

"Ina kira ga shugaban ƙasa ya mayar da hankali kan abin da nake faɗa. Ina son a cire kuɗi daga tasirin siyasa, a saka kuɗi a aljihun jama'a, sannan a samar da tsarin lafiya ga kowa da kowa."

Ya ƙara da cewa Trump ya fi mayar da hankali kan yi masa ba'a maimakon nemo hanyoyin magance matsalolin tattalin arzikin jama'a.

Alkawarin da El-Sayed ya yi

El-Sayed ya ce babban abin da kamfen ɗinsa zai fi mayar da hankali a kai shi ne rage tsadar rayuwa, bunƙasa damar samun ingantaccen kiwon lafiya da kuma magance matsalar gidaje a Michigan.

Kara karanta wannan

Hankalin Trump ya tashi da Musulmi, Abdul El Sayed ya lashe zabe a Amurka

Ya kuma soki abokin hamayyarsa na jam'iyyar Republican, Mike Rogers, yana zarginsa da karɓar fiye da dala miliyan 1 daga kamfanonin magunguna lokacin yana majalisar dokokin Amurka.

Abdul El-Sayed da ya ci zabe a Amurka
Abdul Sayed a wajen yakin neman zabe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Game da tallafin soji ga Isra'ila, El-Sayed ya ce ba ya goyon bayan bai wa kowace ƙasa tallafin soja ba tare da sharadi ba.

Ya bayyana cewa bai dace a riƙa kashe kuɗin harajin Amurkawa wajen tallafa wa rundunonin sojin ƙasashen waje ba, yana mai cewa ya kamata a karkata kuɗin wajen inganta makarantu, kiwon lafiya da abubuwan more rayuwa a cikin Amurka.

China ta sa wa Amurka takunkumi

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin kasar China ta sanar da ɗaukar sababbin matakan tattalin arziki kan Amurka.

Matakan sun haɗa da takaita fitar da jirage marasa matuƙa zuwa Amurka da kuma kakaba takunkumi kan wasu kamfanonin Amurka saboda smatakan da Washington ta ɗauka kan kamfanonin China.

Ana sa ran shugabannin ƙasashen biyu, Xi Jinping da Donald Trump, za su gana a watan Satumba yayin da ake ƙoƙarin rage zaman ɗar-ɗar da ke tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng