Kano Ta Bar Jihohi a baya, Ta Cika Sharadin Inganta Ilimi a Najeriya

Kano Ta Bar Jihohi a baya, Ta Cika Sharadin Inganta Ilimi a Najeriya

  • Jihar Kano ta kere sauran jihohi da ke Arewa maso Yamma bayan ta cika ka’idar 26% na kasafin ilimi a shekarar 2026 a shiyyar
  • Kano ta zama ita kaɗai ce ta cika sharaɗin a yankin da ke fama da karuwar yara marasa zuwa makaranta da masu gararamba a tituna
  • Jihohin Jigawa da Katsina sun yi fice wajen zuba kudi da gyaran tsarin karatun tsangaya duk da an fuskanci kalubale a wajen aiwatar da kasafin 2025

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Binciken kasafin kuɗin shekarar 2026 na jihohin Arewa maso Yamma ya nuna cewa jihar Kano ce ke kan gaba wajen ware kuɗi ga ilimi.

Jihohin Jigawa da Katsina sun kuma sun yi zarra wajen karkata ga zuba jari da gyaran tsarin ilimin karatun tsangaya, da shi ma ke cikin matsaloli iri-iri.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya yi gargadi kan neman hana kamfen a jihohin Arewa 8

Kano ta jagoranci Jihohin Arewa maso Yamma kan kasafin ilimi a 2026
Gwamnonin Arewa maso Yamma a wani taro da suka yi a Kano Hoto: @dikko_radda
Source: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa rahoton ya nuna cewa duk da yawancin jihohi sun ƙara kasafin ilimi, akwai damuwa kan yadda ake aiwatar da kasafin, musamman sakamakon gazawar aiwatarwa a 2025.

Kasafin 2026: Kano ta cika sharadin inganta ilimi

A 2026, Gwamnatin Kano ƙarƙashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware 28.6% na kasafin ta na Naira tiriliyan 1.48 ga ilimi, abin da ya sa ta zama jiha kaɗai da ta cika wannan sharadi.

Haka kuma, ta ware Naira biliyan 2.81 domin ayyukan ilimin tsangaya da suka haɗa da gyaran makarantu, ciyar da ɗalibai da horar da malamai.

Sai dai kuma, aiwatar da kasafin 2025 ya yi ƙasa sosai, wanda ke nuna akwai gibi tsakanin tsare-tsare da aiwatar da abubuwan da aka tsara.

Jihohin Arewa sun yi hobbasa wajen harkar ilimi

A Jigawa, gwamnatin Umar Namadi ta ware 25% na kasafin ta na Naira biliyan 901.84 ga ilimi, kusa da cika sharaɗin da aka ware a ƙasa.

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House

Ta kuma ware Naira biliyan 3.6 ga tsangaya, tare da kafa hukuma ta musamman domin kula da wannan fanni.

Gwamnatin ta ce tana shirin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar haɗa ilimin addini da na zamani, inda sama da yara miliyan 1.3 ke cikin tsarin.

A Kaduna, gwamnatin Uba Sani ta ware 24.7% na kasafin ta ga ilimi tare da shirye-shiryen kan makarantun tsangaya, amma aiwatar da kasafin 2025 ya tsaya a 55%.

Gwamnatin Katsina ta ware 17.2% ga ilimi a kasafin 2026
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Katsina ta ware 17.2% na kasafin ta, ciki har da Naira biliyan 4.33 ga tsangaya—ɗaya daga cikin mafi girma a yankin—duk da cewa aiwatarwa a 2025 ya kai 61.8%.

A Kebbi, an ware 10.9% kacal ba tare da b tare da bayyana shiri kan tsangayaba, duk da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Sakkwato ta ware 13.6% tare da kafa hukumar kula da almajirai da ayyukan Naira miliyan 851.5, amma aiwatar da kasafin 2025 ya yi rauni sosai.

Zamfara kuwa ta ware mafi ƙanƙantar kaso, wato 7.5%, duk da tanadin Naira biliyan 1 ga shirye-shiryen ilimin tsangaya, inda matsalar ƙarancin kuɗi ke hana cikakken aiwatar da kasafin.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Fintiri da gwamnonin Arewa 7 da za su bar mulki nan da shekara 1

Gwamnatin Kano ta fara inganta ilimi

A baya, mun ruwaito cewa Gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana kan bakarta na tabbatar da dawo da martabar ilimi a dukkanin sassan jihar.

Gwamnatin ta ce zuwa yanzu, ta gyara fiye da makarantu 1,200 a ƙananan hukumomi 44, bayan haka kuma ta yi gyara a sassan Kano mai ƙananan hukumomi 44.

Haka kuma ta ware N3bn don gyaran makarantu 13 na ’yan mata da aka rufe a baya, a wani yunkuri na dawo da darajar ilimi a jihar, musamman na yara mata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng