Tunawa da Tsohon Shugaban Najeriya, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, in Ji Aminu Tambuwal

Tunawa da Tsohon Shugaban Najeriya, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, in Ji Aminu Tambuwal

  • Tsohon gwamnan na Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya shaidi marigayi Umaru Musa Yar'adua a matsayin shugaba mai mutunta doka
  • Tambuwal, a jawabin tunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, ya ce mutuwar 'Yar'aduwa ta sauya yanayin siyasar kasar nan
  • A ranar 5 ga watan Mayun 2010, Allah ya karbi rayuwar shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, bayan fama da rashin lafiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar 5 ga watan Mayun 2010, Allah ya karbi rayuwar shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, bayan fama da rashin lafiya.

A rayuwa, wasu lokuta kan zamo abin tunawa, yayin da wasu lokutan kan zamo tarihi wanda ba zai mantu ba, a cewar Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Kara karanta wannan

Kwanaki kusan 7 da kammala taro a kasar Saudi, shugaba Tinubu bai dawo Najeriya ba

Aminu Tambuwal ya yi jimamin mutuwar Umaru Musa Yar’Adua
Aminu Tambuwal ya shadi tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa 'Yar'Adua. Hoto: @AWTambuwal
Asali: Twitter

Tambuwal, a shafinsa na Twitter, ya ce ranar 5 ga Mayu, 2010 ta kasance abar tunawa ga Nijeriya da al’ummarta, kuma ta shiga tarihi na har abada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal ya tuna da mutuwar 'Yar'aduwa

A irin wannan ranar, shekaru 14 da suka gabata, mai kishin dimokradiyya kuma shugaba na gari, Mai Girma Umaru Musa 'Yar'aduwa GCFR, mutun mai tawali'u, hangen nesa, manufa mai kyau, ya shaki numfashinsa na karshe.

"Wannan rana mai cike da juyayi ta sauya yanayin siyasar kasarmu, ta bar wani gibi da zai yi matukar wahalar cikawa."

- In ji Sanata Tambuwal.

Tsohon gwamnan na Sokoto, ya shaidi marigayi Shugaba 'Yar'aduwa da zama mutum mai hazaka da kuma matukar mutunta doka.

"Yar'aduwa jigon siyasa ne" - Tambuwal

Sanata Tambuwal ya ce:

"Yar'aduwa ya kasance mai kishin kasa wanda ya yi imani da samar da tsarin dimokuradiyya mai kyau, kuma ya dukufa wajen samar da hadin kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Sarkin Musulmi ya fadi abin da talakawa za suyi wa shugabanni

"Ya kasance jigon siyasa a gare ni da wasu da yawa waɗanda suka yi imani da gina cibiyoyi da tsare-tsare masu ƙarfi maimakon dogaro ga wasu mutane 'yan kalilan masu ƙarfin fada aji."

Tsohon gwammnan ya shiga sahun 'yan Najeriya wajen mika sakon ta'aziyya, alhini da kuma tunawa da "wannan hazikin mutum mai yakana da hangen nesa."

Karanta jawabin a kasa:

Tinubu zai yi koyi da 'Yar'Adua

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito shugaban kasa Bola Tinubu ya jinjinawa marigayi Umaru Musa 'Yar'Adua tare da cewa zai yi koyi da shi.

Tinubu, a sakon cika shekaru 13 da rasuwar marigayi Yar'adua, ya bayyana shi ba matsayin mutum mai gaskiya da jajircewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel