Amnesty Ta Ce Fulani 150 Sun Mutu a Kwara bayan Sun Sha Azaba
- Kungiyar Amnesty International da ke rajin kare hakkin dan Adam ta yi zargin cewa akalla Fulani 150 ne suka mutu a wani sansani a Kwara
- Ta bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta bincike domin daukar mataki a kan duk wanda aka samu da laifi wajen jawo mutuwar mutanen
- Gwamnatin jihar Kwara ta yi magana game da lamarin, haka zalika rundunar sojin Najeriya ta taba magana game da sansanin da aka killace Fulanin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - Kungiyar Amnesty International ta yi zargin cewa akalla mutane 150 'yan kabilar Fulani, ciki har da yara, sun mutu a wani wurin tsare mutane Jihar Kwara.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar Amnesty ta bukaci hukumomin Najeriya da su fara bincike mai zaman kansa cikin gaggawa game da lamarin.

Source: Facebook
Amensty: 'Fulani 150 sun mutu'
A cikin wata sanarwa da ta fitar a X, Amnesty ta ce wadanda suka mutu na daga cikin kusan makiyaya 1,500 da aka raba da muhallansu, wadanda aka killace a sansanin horaswa na NYSC da ke Yikpata.
Ta bayyana cewa an killace su a sansanin ne bayan sun tsere daga hare-haren tashin hankali a wasu sassan Jihar Kwara.
A cewar Amnesty, wadanda aka tsare sun fuskanci cunkoso da rashin kulawa, tare da karancin abinci, matsalolin kiwon lafiya da sauransu, lamarin da ya haifar da yunwa da cututtuka masu yawa.
“Fulani sun fuskanci tsanantawa ta fuska biyu, daga kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma sojoji,”
In ji Isa Sanusi, shugaban Amnesty International na Najeriya.
Me Amnesty ta dogara da shi?
Kungiyar ta ce bincikenta ya biyo bayan nazari da ta gudanar tsakanin 5 zuwa 11 ga Afrilun 2026, inda tawagarta ta tattauna da dama daga cikin wadanda aka tsare, wadanda suka tsira da kuma iyalan da abin ya shafa.
Ta kara da cewa hotunan da aka samu daga sansanin sun nuna yara cikin tsananin yunwa, inda kasusuwa ke fito musu a fili da kuma rauni mai tsanani.
Amnesty ta ce wadanda suka tsira sun bayyana halin da suka fuskanta a sansanin a matsayin mai tsanani, ciki har da yawan mace-mace da kuma birne gawa da yawa a lokaci guda.
Wasu daga cikin wadanda Amnesty ta tattauna da su sun ce sun bar gidajensu da dabbobinsu a Janairu 2026 bayan hukumomi sun umarci mazauna da ake ganin ba su da laifi da su fice daga kauyukansu domin gudanar da aikin tsaro.
An bayyana cewa lamarin ne ya sa daruruwan mutane suka taru a wani wurin da aka ware. Daga nan ne aka kwashe su da motocin soja zuwa sansanin Yikpata, inda aka tsare su na dogon lokaci.

Source: Original
Amnesty ta kara da cewa wani mutum mai shekaru 43 da ya tsere daga sansanin ya ce mace-mace na faruwa akai-akai.
“Jimillar mutane 154 sun mutu sakamakon yunwa da cututtuka tun lokacin da aka kawo mu. A ranar da na tsere, yara shida sun mutu,”
In ji shi.
Martanin rundunar sojin Najeriya
Da ta ke mayar da martani kan zargin, Hedikwatar Tsaro ta yi watsi da rahoton, tana mai cewa wurin ba mallakin soja ba ne.
Daraktan ayyukan watsa labarai na rundunar tsaro, Michael Onoja, ya bukaci Daily Trust ta tuntubi wasu hukumomin gwamnati.
Onoja, Manjo Janar, ya ce:
“Labarin ba gaskiya ba ne.
“Sojoji ba su da wata alaka da wannan wuri. Ku tuntubi hukumomin da suka dace domin karin bayani.”
Martanin gwamnatin Kwara
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Jihar Kwara ta musanta cewa tana da hannu a gudanar da irin wannan sansani.
Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bashir Adigun, ya ce gwamnatin jihar ba ta da iko a kan wurin.
“Gwamnatin jihar ba ta da wani sansani,”
In ji shi, yana mai cewa sojoji ne suka fi dacewa su mayar da martani kan zargin.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar Operation Savannah Shield, Kyaftin Mohammed Jamilu Yahaya, ya ce zai bincika zargin.
Amnesty ta zargi Abba Kabir
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Amnesty International ta zargi gwamna Abba Kabir Yusuf da kuntatawa 'yan adawa a jihar Kano.
Ta jero wasu 'yan jam'iyyun adawa da ta ce an kama su saboda fadin albarkacin bakinsu game da yanayin siyasar jihar da kuma gwamnan.
Kungiyar ta ce babu wanda ya kamata a hana sukar gwamnati, domin a cewarta sukar kowace gwamnati na cikin damar da dimokurdiyya ta bayar.
Asali: Legit.ng



