An kashe Fulani 32 a wani rikicin kabilanci

An kashe Fulani 32 a wani rikicin kabilanci

Kashe - kashe dai ya zama tamkar ruwan dare a duniya, inda a yanzu haka an kaiwa Fulani wani mummunan harin kabilanci an kashe musu mutane 32

An kashe Fulani 32 a wani rikicin kabilanci

An kashe Fulani 32 a wani rikicin kabilanci

Kimanin mutane 32 ne suka sheka lahira a sakamakon wani rikici na kabilanci da ya barke a yankin Mopti dake kasar Mali.

DUBA WANNAN: An kashe mutane 3, sannan an sace matar sarki a wata jiha a Najeriya

A sanarwar da kafar yada labarai ta kasar suka fitar, sun nuna cewa, wasu mutane dauke da muggan makamai 'yan kabilar Dogon sune suka kai wannan mummunan hari akan al'ummar kauyen Koumaga wadanda su kuma kabilar Fulani ne makiyaya dake a jihar ta Mopti.

Hukumomin kasar sunce, har ya zuwa yanzu an nemi wasu mutane uku kuma an rasa su.

Rahotanni sun nuna cewar ana yawan samun matsalar rashin tsaro a jihar ta Mopti wacce ke tsakiyar kasar ta Mali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel