Duk da Allah Wadan Abba, Matar da Ta Jagoranci Ɗaga Kamfai Ta Samu Mukami a Kano
- Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano, Yusuf Imam (Ogan Boye), ya naɗa Fatima Naseer, a matsayin mai kula da harkokin mata
- Teemahcool ita ce matar da ta jagoranci gangamin ɗaga ɗan kamfai domin yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso ba’a a lokacin ziyarar uwargidan Bola Tinubu
- Wata wasiƙar naɗi da sakataren ƙaramar hukumar, Ado Mohammed Hotoro, ya sanya wa hannu, ta bayyana dalilin nadin Fatima bayan dambarwar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano – Fatima Naseer Teemahcool, shahararriyar matashiyar nan da ke yin bidiyoyi a dandalin TikTok, ta samu damar shiga cikin sahun masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar Kano.
Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Yusuf Imam Ogan Boye, ne ya amince da naɗin nata a matsayin jami’ar da za ta lura da sha’anin mata a ƙaramar hukumar.

Source: Facebook
'Yar TikTok ta samu mukamin gwamnati a Kano
Wannan nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ado Mohammd Hotoro, Sakataren karamar hukumar ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, 30 ga Afrilun 2026, in ji rahoton Daily Trust.
Sanarwar ta bayyana cewa Yusuf Ogan Boye ya dauki wannan mataki ne sakamakon kishin da Fatima take da shi ga ci gaban karamar hukumar Nasarawa.
Yusuf Imam Ogan Boye, ya umurci Teemahcool ta da ta gudanar da ayyukanta daidai da ƙa’idoji da dokokin da suka shafi gudanar da ƙaramar hukumar.
Abubuwan da suka ja hankali kafin nadin mukamin
Naɗin Fatima Teemahcool ya haifar da kace-nace a kafafen sada zumunta, duba da cewa a makon jiya ne ta fuskanci kakkausan suka bayan jagorantar nuna dan kamfai a lokacin ziyarar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, a Kano.
Wannan abin da aka yi shi domin tsokana ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya janyo mata Allah-wadai daga sassa daban-daban na jihar.

Kara karanta wannan
Tirkashi: EFCC ta fara farautar babbar jagora a kungiyar yakin neman zaben Tinubu
Sai dai Fatima ta fito fili ta ba da haƙuri, inda ta yi alƙawarin ba za ta sake aikata hakan ba, kamar yadda rahoton jaridar Aminiya ya nuna.
Ita ma gwamnatin jihar Kano ta nisanta kanta da ɗaga wannan kamfai, inda ta bayyana cewa hakan ya saɓa wa al’ada da kuma koyarwar addinin Musulunci.

Source: Facebook
Gudunmawar Teemahcool a siyasa
Teemahcool ta kasance ɗaya daga cikin fitattun matasan da suka yi fafutuka a lokacin yaƙin neman zaɓen gwamna da kuma na shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa.
Ta kasance mai nuna goyon baya ga Ogan Boye tun daga matakin neman zaɓe har zuwa lokacin da ya samu nasara, wanda hakan ya sa masu sharhi ke kallon wannan muƙami a matsayin tukuicin siyasa.
Abba ya yi tir da ɗaga ɗan kamfai
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf, ya ce ba shi da hannu a zargin da ke yawo na cewa gwamnatinsa ta raba dan kamfai ga mata a matsayin tallafi.
Yayin da yake Allah wadai da gangamin daga dan kamfan, da aka jingina masa shi, Abba ya ce an raba dan kamfai din ne ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.
Gwamnan Kano ya bayyana cewa bayan ya samu cikakken bayani, nan take na gayyato ‘yan matan da suka nuna dan kamfai a Kano, ya yi masu fada tare da nuna masu kuskurensu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
