An Kunyata 'Yan Jarida a Zaman Shari'ar Wadanda Ake Zargi da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya

An Kunyata 'Yan Jarida a Zaman Shari'ar Wadanda Ake Zargi da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya

  • Alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta kori 'yan jarida a zaman shari'ar wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki
  • Wannan mataki ya fito ne daga jami'an tsaro yayin da suka fattaki duka 'yan jaridar da suka yi sammako, suka shiga kotun a Abuja
  • A yau Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026 ne kotun ta tsara ci gaba da zama kan mutane shida da gwamnatin tarayya ta gurfanar a makon jiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An kori ‘yan jarida daga dakin shari'a na 6 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yayin zaman sauraron shari’ar mutane shida da ake zargi da shirin kifar da gwamnatin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan jarida sun isa kotun tun da misalin karfe 8:00 na safiyar yau Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026, inda suka zauna a layin baya suna jiran fara zaman kotu.

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman shari'a a kotunan Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

The Nation ta ruwaito cewa kafin karfe 9:00 na safe, wani jami’in kotu ya sanar da cewa duk wanda bai samu kujera ba ya fita, domin alkalin ba zai amince a tsaya a tsaye ba yayin zaman.

An kori yan jarida daga cikin kotu

Sai dai yayin da wasu ke fita, jami’an tsaro da ke aiki a kotu suka umarci ‘yan jarida su tashi su fice gaba daya daga dakin zaman kotun.

Lokacin da aka tambaye su dalili, jami'an tsaro sun ce umarni ne daga alkalin kotun, Mai shari’a Joyce Abdulmalik, wadda ta hana ‘yan jarida shiga zaman.

Ko da aka nuna musu cewa shari’ar na da muhimmanci ga jama’a kuma babu wani umarnin kotu da ya hana dauko rahoton zaman, jami’an sun nace kan aiwatar da umarnin alkalin.

Bayan fitar da ‘yan jarida, an kulle kofar kotun sannan aka fara zaman shari’ar kamar yadda aka tsara, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Yadda gwamnati ta gurfanar da mutum 6

Idan ba ku manta ba gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu mutane shiga gaban kotu a makon jiya bisa zargin hannu a yunkurin yi wa shugaban kasa, Bola Tinubu juyin mulki.

Mutanen shida da ake tuhuma sun hada da Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya, Kyaftin Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya, Sufeto Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a fadar Aso Rock, Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tuhume-tuhumen da ake yi wa mutanen

An gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume guda 13 da suka hada da yunkurin tada yaki da gwamnatin tarayya domin tsoratar da Shugaban kasa da kuma cin amanar kasa.

Ana zargin su da hada baki domin kifar da gwamnati, aikata ta’addanci, boye bayanan tsaro da kuma safarar kudaden da ake dangantawa da tallafa wa ta’addanci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano da makamai cikin dare, sun yi kisa

Rahotanni sun nuna cewa babbar kotun tarayya ta shiga zaman sauraron wannan shari'a yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja.

Kotu ta mika wadanda ake zargi hannun DSS

A baya, kun ji cewa babbar kotun tarayya ta umarci hukumar DSS ta tsare mutane shida da aka gurfanar gabanta bisa zargin kitsa juyin mulki a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wadanda ake zargin ne kan tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci da cin amanar kasa.

Bayan gurfanar da su, bangaren gwamnatin tarayya ya bukaci kotu da ta bayar da umarnin tsare su a hannun hukumar DSS tare da gaggauta fara shari’ar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262