Juyin Mulki: Tijjaniya Ta Tayar da Maganar Zargin Sheikh Khalifa, Ta Ja Kunnensu

Juyin Mulki: Tijjaniya Ta Tayar da Maganar Zargin Sheikh Khalifa, Ta Ja Kunnensu

  • Ƙungiyar Tijjaniyya ta shawarci miliyoyin mabiyanta yayin da ake ci gaba da tuhumar Sheikh Abdulkadir Sani Khalifa da ake yi
  • Ta bukace su da su kauce wa furuci da zai iya dagula shari’ar Malamin da ake yi kan zargin hannu a juyin mulki
  • An gurfanar da Sheikh Khalifa kan zargin shirin juyin mulki da ta’addanci, inda ya musanta tuhume-tuhume 13

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Ƙungiyar darikar Tijjaniyya ta yi magana game da ci gaba da tuhumar Sheikh Abdulkadir Sani Khalifa da ake yi kan hannu a juyin mulki.

Ƙungiyar ta bukaci mabiyan ta a Najeriya da su guji yin kalamai da za su iya kawo cikas ga shari’ar malamin da ke gudana a kotu.

An shawarci yan Tijjaniya kan zargin Sheikh Khalifa
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zariya. Hoto: Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da Daily Trust ta samu, mataimakin shugaban majalisar shura ta Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, ya buƙaci mabiya su dage da addu’o’i domin samun nasarar malamin.

Kara karanta wannan

Tsohon sufeta janar ya zargi APC da neman hana shi takarar gwamna

Musabbabin kama Sheikh Khalifa Zaria

An kama Sheikh Khalifa kusan watanni biyar da suka gabata, sannan aka gurfanar da shi a makon da ya wuce bisa zargin shirya juyin mulki a kan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhume 13 da aka karanta masa a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka ɗage shari’ar domin fara sauraron ƙarar.

Ƙungiyar Tijjaniyya ta bayyana cewa tana da yaƙinin kotu za ta wanke Sheikh Khalifa, kamar yadda a baya wata kotu ta bayar da umarnin a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba.

An gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a juyin mulki
Sheikh Abdulkadir Sani Khalifa, Timipre Sylva da Kanal Mohammed Ma'aji. Hoto: Zawiyar Sheikh Sani Khalifa Zaria, Timipre Sylva, Zagazola Makama.
Source: Facebook

An bayyana halayen Sheikh Khalifa Zariya

Sanarwar ta jaddada cewa Sheikh Khalifa fitaccen malamin addini ne wanda aka san shi da koyarwa mai zaman lafiya da kuma kira ga bin doka da oda a cikin al’umma.

Ta kuma bayyana yadda aka kama shi a hedikwatar bankin Ja’iz da ke Abuja bayan an dakatar da asusunsa, inda jami’an tsaro suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan bindigogi da wukaken da aka so kashe Trump da su

Hakan ya jefa iyalansa da mabiya darikar cikin damuwa, musamman ganin cewa ya shafe watanni ba tare da ganawa da lauyoyinsa ko iyalansa ba har sai bayan an mayar da shi hannun DSS.

Daga baya, kotu ta yanke hukuncin cewa an take masa haƙƙoƙinsa, tare da umartar a sake shi da kuma cire takunkumin da aka sanya a asusun bankinsa.

Sai dai gwamnatin tarayya ta sake shigar da ƙara a kansa da wasu mutane biyar kan zargin ta’addanci, inda aka fara shari’ar a gaban kotu.

Ƙungiyar Tijjaniyyar ta buƙaci mabiya ta su kasance masu haƙuri da bin doka, tare da yin addu’o’i domin samun nasara a shari’ar da ke gudana, cewar Leadership.

Iyalan Sheikh Khalifa sun karyata labarin mutuwarsa

An ji cewa iyalan Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa Zariya sun yi karin haske kan halin da yake ciki lokacin da ake ta yada jita-jitar rasuwarsa.

Ɗansa mai suna Ibrahim ya bayyana cewa an hana malamin ganawa da lauyoyi kuma hukumomi ba su ba su wani bayani ba kan binciken ba.

Iyalan sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta gurfanar da shi a kotu idan akwai zargi tare da ba su damar ganin mahaifinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.