Majalisar Dattawa Ta ba Tinubu Damar Ciyo Bashin Dala Miliyan 516 daga Kasar Waje
- Majalisar dattawa ta sahalewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbo bashin Dala miliyan 516 domin gina titin Sokoto zuwa Badagry
- Hakan dai na zuwa ne bayan kwamitin kula da basussukan gwamnati na Majalisar dattawa ya mika rahotonsa a zaman yau Laraba
- A ranar Talata da ta gabata ne Majalisar wakilai ta amince da karbo wannan rance, wanda ake ganin zai kara hada Kudu da Arewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu ta karbo rancen Dala miliyan 516 domin gina kashi na farko na titin Sokoto zuwa Badagry.
'Amincewar ta biyo bayan nazari da Majalisar dattawan ta yi kan rahoton kwamitin kula da basussukan cikin gida da na waje, karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko ya gabatar.

Source: Facebook
Kwamiti ya mika rahoto ga Majalisar tarayya
Kwamitin ya ba da shawarar a saka bashin cikin tsarin basussukan gwamnatin tarayya, kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito.
Rahoton ya nuna cewa bashin yana da garantin kariya daga Hukumar Musulunci ta Inshorar Zuba Jari da Bayar da Lamuni (ICIEC), kuma za a biya shi cikin shekaru tara, tare da wa'adin sassauci na shekaru uku.
Muhimmancin titin Sokoto-Badagry
Yayin muhawara, mambobin majalisar dattawan sun jaddada mahimmancin wannan aiki na titin Sokoto zuwa Badary da ke jihar Legas.
Sanata Tahir Monguno ya bayyana cewa hanyar za ta hada yankuna uku na Najeriya kuma za ta rage wahalhalun tafiya tsakanin Arewa da Kudancin kasar nan.
Haka zalika sanatocin sun bayyana cewa hanyar za ta bunkasa harkar noma ta hanyar saukaka kai amfanin gona kasuwanni da kuma karfafa ayyukan madatsun ruwa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Tinubu ya nemi ciyo wannan bashi ne a madadin wata tsohuwar bukatar karbi aron Dala miliyan 5 da ta samu tangarda.
A cewarsa, bukatar karbo bashin daga Abu Dhabi ta tsaya cak ne sakamakon rikice-rikicen da suka barke a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan ya hana Gwamnatin Tarayya samun kudaden.

Source: Facebook
Majalisa ta amince da bukatar Tinubu
A ranar 23 ga watan Afrilu 2026 ne Shugaba Tinubu ya aike da wasika zuwa ga Majalisar Dattawa don neman amincewarta wajen karbo aron Dala miliyan 516 daga wani banki a kasar Jamus.
Ana sa ran titin mai tsawon kilomita 1,000 zai ratsa jihohin Sokoto, Kebbi, Niger, Kwara, Oyo, Ogun da Lagos, daga Illela zuwa Badagry.
Gwamnatin tarayya za ta bayar da sama da naira biliyan 265 domin biyan kudin filaye da sauran abubuwan da suka shafi aikin.
Ana sa ran majalisar dattawan za ta aika da amincewar ga Shugaban kasa domin daukar mataki na gaba, yayin da majalisar wakilai ta riga ta amince da bukatar a ranar Talata, cewar rahoton Daily Trust.
Majalisar Dattawa ta amince da nadin minista
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da nadin Muttaqa Rabe Darma wanda ya fito daga jihar Katsina a matsayin Ministar Gidaje da Raya Birane na Tarayya.
Da yake jawabi a gaban sanatoci, Muttaqa Rabe Darma, ya yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da majalisar dokoki ta kasa domin magance ƙarancin gidaje a Najeriya.
Ya lura cewa fiye da ‘yan Najeriya miliyan 100 ne matsalar ƙarancin gidaje ta shafa, sannan ya jaddada buƙatar sanya gidaje su kasance masu sauƙin samu da rahusa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


