Kotu Ta Daga Shari'ar Masarautar Kano Zuwa bayan Zaben 2027
- Rahotanni sun nuna cewa Kotun kolin Najeriya ta dage shari'ar da ta ke yi game da dambarwar masarautar Kano zuwa bayan zaben 2027
- Aminu Babba Danagundi da ya shigar da kara ya yi karin bayani game da dalilin da ya sanya aka daga shari'ar zuwa lokaci mai tsawo
- Lauya mai kare majalisar Kano, Barista Bashir Muhammad Tudun Wuzirchi ya yi karin haske game da halin da ake ciki a kan shari'ar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kotun koli ta sanya ranar 19 ga Afrilun 2027 a matsayin sabuwar ranar cigaba da sauraron shari'ar da aka shigar gabanta game da masarautar Kano.
Ta sanya ranar ne domin sauraro tare da karɓar martanin masu ƙara a shari'ar wadda Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar gabanta.

Source: Twitter
Rahoton da Premier Radio ya wallafa a Facebook ya nuna cewa Dan Agundi yana ƙalubalantar hana shi damar da doka ta ba shi a matsayinsa na babban ɗan majalisar Sarki.
Dalilin daga shari'ar masarautar Kano
Yayin da ya ke karin haske kan shari'ar, Dan Agundi ya ce sun dauka za a gama shari'ar gaba daya, amma sai lauyan gwamnati ya kawo korafi a ranar 18 ga watan Afrilun 2026, saboda haka aka daga shari'ar zuwa wani lokaci.
A wani bidiyo da Arewa Updates ta wallafa a Facebook, Dan Agundi ya ce:
"Mun dauka yau za a je shari'a gaba daya, amma sai lauyoyinsu suka kawo korafi."
Dan Agundi ya bayyana cewa dama kotun koli na daga shari'a zuwa lokaci mai tsawo amma aka kai su zuwa watan Afrilun 2027, wanda bai yi nisa sosai ba.
A kan haka ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta yi ya yi daidai, inda a yanzu haka aka ba su lokacin da za su yi nazari kan korafin da layoyin gwamnati suka shigar domin su yi martani.
Ya kara da cewa babba abin da suke nema shi ne a rusa hukuncin da majalisar Kano ta yi game da masarautun jihar, wanda zai shafi duk wani hukunci da aka yi a bayan shi.

Source: Facebook
Bayanin lauyan gwamnatin Kano
Lauyan waɗanda aka yi ƙara a shariʼar, Barista Bashir Muhammad Tudun Wuzirchi ya yi ƙarin bayani kan yadda zaman kotun koli ya kasance.
Baristan ya bayyana cewa babu sunan Mai martaba Muhammad Sanusi II ko Mai martaba Aminu Ado a shari'ar, domin Babba Dan Agundi ne ya shigar da majalisar Kano da sauransu kara.
Lauyan ya ce masu shigar da kara sun yi korafi da cewa a ba su sabuwar rana domin su mayar da martani kan wani korafin da aka yi game da shari'ar.
Ya kara da cewa shari'ar ba ta da alaka da waye Sarkin kano, ya ce ana shari''ar ne a kan ko kotun na da 'yancin sauraron abin da ya shafi lamuran shari'ar sarautar jiha.
Ga bibiyon bayanin da lauyan ya yi a kasa:
An yi rashi a masarautar Bida
A wani labarin, mun kawo muku cewa an wayi gari da labarin rasuwar Son Fada na Etsu Nupe a jihar Neja wato Mahmud Abubakar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai farmaki fada, sun yi garkuwa da mai martaba Sarki a Najeriya
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya mika sakon ta'aziyya ga masarautar Bida, Etsu Nupe da al'ummar jihar baki daya game da rashin.
Bago ya ce marigayin ya kawo cigaba sosai kuma tarihi zai cigaba da tunawa da shi, inda ya roki Allah ya gafarta masa kurakuran shi.
Asali: Legit.ng

