'An Saka Tallafi a Man Fetur domin Rage Farashi a Najeriya,' Jami'in Matatar Dangote
- Wani jami'in matatar Dangote da ke Legas ya bayyana cewa ana saka tallafi a man fetur da dizil da suke sayarwa domin rage farashinsu
- Hakan na zuwa ne yayin da yakin da aka yi tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran ya dagula kasuwar makamashi a duniya, lamarin da ya shafi Najeriya
- Jami'in ya yi bayani kan farashin man jirgin sama da ya tashi sosai, inda kamfanonin sufuri suka yi barazanar daina aiki a fadin kasar nan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wani babban jami’in matatar Dangote ya bayyana cewa suna sayar da fetur da dizal a Najeriya ne a farashi mai sauki da ke dauke da tallafi domin saukakawa jama’a.
A cewarsa, farashin N1,200 kan kowace lita na fetur da kamfanin ke sayarwa ya yi kasa da yadda kasuwa ke tafiya a halin yanzu, musamman bayan tashin farashin danyen mai sakamakon rikicin Amurka da Iran.

Source: Getty Images
Rahoton Punch ya nuna cewa rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya ya janyo tashin farashin mai, bayan Iran ta toshe mashigar ruwa ta Hormuz.
Sakamakon haka, matatar Dangote ta kara farashin fetur daga N774 zuwa N1,200 a lita. Haka kuma karin farashin ya shafi dizal da man jirgin sama.
An saka tallafin man fetur
Jami’in na matatar Dangote ya ce duk da cewa an saka tallafi a farashin fetur da dizal gwargwadon iko domin taimakawa jama’a, ba za su iya rage farashin man jirgin sama ba.
Saboda haka, ya bayyana cewa ana sayar da man jirgin sama ne bisa farashin kasuwa da yadda lamura ke gudana ba tare da wani tallafi ba.
Ya danganta tashin farashin man fetur da dizal da hauhawar farashin danyen mai a duniya.
Ya ce:
“Bayan tashin farashin danyen, mun rage farashin fetur gwargwadon iko domin taimakawa jama’a. Haka ma dizal mun yi kokarin saukakawa kadan.
"Amma ba za mu iya rage farashin komai ba, shi ya sa muke sayar da man jirgin sama bisa yadda kasuwa take.”
Domin kaucewa rudani, jami’in matatar ya amince cewa kalmar “rage farashi” da ya yi amfani da ita na nufin saka tallafi a bagarorin fetur da dizal.

Source: Facebook
Batun farashin man jirgin sama
Wani jami’i daban na rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana cewa kamfanin na sayar da man jirgin sama ga ‘yan kasuwa kasa da N2,000 a kowace lita.
Ya ce:
“Zan iya tabbatar maka cewa a safiyar Litinin farashin man jirgin sama da muke sayarwa ya kai N1,799. A baya ma ya fi haka sauki. Wannan shi ne farashin da muke bai wa ‘yan kasuwa, su kuma su sayar wa kamfanonin jirage.”
Man jirgin sama ya tashi sosai
A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan kasuwa da kungiyoyin sufuri sun koka kan yadda farashin man jirgin sama ya tashi a Najeriya.
Wata kungiya ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani domin daidaita farashin saboda kaucewa matsala a lokacin zuwa aikin Hajji.
Kungiyar ta ce tashin farashin zai iya shafar ribar da kamfanonin jiragen sama za su iya samu da yadda za su jagoranci zuwa da dawowar mahajjata.
Asali: Legit.ng

