Kurunkus: An Gurfanar da Mutane 6 da Ake Zargi da Yunkurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

Kurunkus: An Gurfanar da Mutane 6 da Ake Zargi da Yunkurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

  • A karshe, gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutane shida gaban kotu bisa zargin su da hannu a yunkurin kifar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya jagoranci gurfanar da mutanen yau Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Tsohon karamin ministan harkokin man fetur, Cif Timipre Sylva, wanda ke cikin wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin, bai halarci zaman kotun ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban kotu bisa zargin kitsa juyin mulki da nufin hambarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da wadanda ake zargin a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026 kan tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci da cin amanar kasa.

Kara karanta wannan

Bayan 'sallamar' mutum 2, an kara samun ministan da ya yi murabus a gwamnatin Tinubu

Kotun tarayya.
Dakarun yan sanda a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin Tinubu ta gurfanar da mutum 6

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Antoni Janar na tarayya kuma Ministan shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya jagoranci gurfanar da wadanda ake tuhumar gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

A zaman kotun, wanda ya fara da misalin karfe 1:46 na rana, Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya sanar da kotu cewa an shirya tuhume-tuhumen gaba daya kuma ya nemi izinin a karanta wa wadanda ake kara.

Wadanda ake zargi sun musanta a kotu

Sai dai bayan karanto duka tuhume-tuhumen a gaban kotu, wadanda ake tuhuma mutum shida sun musanta laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan tsawon lokacin da aka shafe ana bincike kan zargin wasu jami'an sojojin Najeirya da fararen hula da kitsa yadda za a kifar da Shugaba Tinubu.

Labarin yunkurin juyin mulkin ya fara yaduwa ne tun a watan Satumba, 2025, inda a farko gwamnatin Najeriya ta musanta kafin daga bisani ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya sa labule da Goodluck Jonathan bayan sukar 'yan adawa

Gwamnatin ta sha alwashin gurfanar da duk wanda aka kama da hannu a kitsa juyin mulkin domin ya gurbi abin da ya shuka bisa tanadin doka.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya Hoto: @OfficialABAT/X
Source: Twitter

Tsohon minista bai halarci zaman kotu ba

Tsohon ministan man fetur da ya yi aiki a gwamnatin marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Timipre Sylva na cikin wadanda ake zargi da hannu a kitsa juyin mulkin.

Sai dai Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa ba ya cikin wadanda gwamnatin tarayya ta gurfanar a gaban kotu yau Laraba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnatin Tarayya ta sake gano bayanai

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta gano yadda wadanda ake zargi da kitsa hambarar da Shugaba Bola Tinubu suka kasafta makudan kudade a tsakanin su.

Bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun karɓi kuɗi masu yawa da ake zargin na tallafin ta’addanci ne, ciki har da Naira miliyan 50, Naira miliyan 10 da sauransu.

Gwamnatin tarayya ta zargi waɗannan mutane da laifuffuka da suka haɗa da cin amanar ƙasa, ta’addanci, ɓoye bayanan tsaro da kuma safarar kuɗaɗen da ake dangantawa da ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262