Babban Lauya Ya Hango Haramci a Shari'a da Sojojin da Suka Shirya Kifar da Tinubu
- Fitaccen lauya a Najeriya, Femi Falana SAN ya bukaci gwamnatin tarayya ylts dakatar da shari’ar da ake yi wa wadanda ake zargi da shirin juyin mulki
- Babban lauya ya ce kotun soji ba ta da hurumin sauraron irin wadannan laifuffuka waɗanda suka danganci yunkurin kifar da gwamnati
- Ya bayyana maganin da ya dace gwamnatin tarayya da dauka kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta tsara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
JihaLagos – Fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya bukaci Ministan shari’a, Lateef Fagbemi, da ya dakatar da shari’ar da ake yi wa sojoji 36 da ake zargi da kitsa juyin mulki a gaban kotun soji.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Falana ya roki AGF da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi a karkashin sashe na 174 domin soke karar da ya bayyana a matsayin “haramtacciya”.

Kara karanta wannan
Ningi: Babban kuskuren da zai hana wasu sanatoci da 'yan majalisu koma wa kujerunsu a 2027

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa cewa Femi Fani SAN ya bayyana cewa dokar Najeriya ba ta amince a yi irin wannan shari'a a kotun soji ba.
Babban lauya ya shawarci gwamnati
Daily Nigerian ta wallafa cewa Femi Falana ya ce akwai kotun da dokar Najeriya ta amince a kai wa irin wannan zargi
Ya ce:
“Na ga ya dace in bukaci Babban Lauyan Tarayya da Ministan Shari’a ya yi amfani da ikon da Sashe na 174 ya ba shi na kundin tsarin mulki domin dakatar da wannan karar da ake yi a gaban kotun soji. Bayan haka, ya kamata a gurfanar da jami’an sojin 36 din a gaban babbar kotun tarayya."
Falana ya jaddada cewa kotun tarayya ce kawai ke da hurumin sauraron laifuffuka kamar cin amanar kasa da kuma yunkurin aikata hakan, yana mai dogaro da tanadin sashe na 251 na kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Babban lauya ya magantu kan dokar ƙasa
Lauyan ya kuma soki yadda ake shirin gurfanar da wasu daga cikin wadanda ake zargi a kotun farar hula, yayin da wasu kuma ake kai su kotun soji kan laifi guda. Ya ce hakan ya saba da ka’idar daidaito a gaban doka.

Source: Twitter
A cewarsa:
“Tun da kundin tsarin mulki ya tabbatar da daidaito a gaban doka, ba za a iya kare shirin gurfanar da mutum shida a gaban babbar kotun tarayya ba, sannan a kai wasu 36 kotun soji kan laifi guda ba."
Falana ya kara da cewa kotun soji ba ta da cikakken ikon shari’a wajen sauraron laifuffukan da suka shafi ta’addanci, cin amanar kasa da makamantansu a tsarin dimokuradiyya na yanzu.
Ya kuma kawo misalai daga tarihi, inda ya bayyana cewa ko a lokacin mulkin soja, ba a taba shari’ar masu yunkurin juyin mulki a kotun soji ba, sai dai a kotunan musamman da aka kafa bisa dokoki na musamman.
An kai mutane 6 kotu kan juyin mulki
A baya, mun wallafa cewa a karshe, gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutane shida gaban kotu bisa zargin su da hannu a yunkurin kifar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya jagoranci gurfanar da mutanen yau Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Tsohon karamin Ministan harkokin man fetur, Cif Timipre Sylva, wanda ke cikin wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin, bai halarci zaman kotun ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
