Majalisa Na Shirin Tsige Gwamna a Najeriya? An Ji Yadda Zancen Yake

Majalisa Na Shirin Tsige Gwamna a Najeriya? An Ji Yadda Zancen Yake

  • Majalisar dokokin jihar Oyo ta yi martani kan batun da ake yadawa wanda ke nuna cewa tana shirin tsige Gwamna Seyi Makinde da shugabanta
  • A yayin zamanta na ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026, majalisar ta kada kuri'ar amincewa da Gwamna Seyi Makinde da shugabanta, Adebo Ogundoyin
  • Majalisar ta bayyana cewa batun shirin tsige Gwamna Seyi Makinde zance mara tushe wanda yake da nasaba ta siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Majalisar dokokin jihar Oyo ta kada ƙuri'ar amincewa da Gwamna Seyi Makinde da shugaban majalisar Adebo Ogundoyin.

Majalisar dokokin ta kuma yi watsi da rahotannin da ke zargin akwai wani shiri na tsige su da ake yi a jihar.

Majalisar dokokin Oyo ta musanta batun tsige Gwamna Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a wurin taro Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Jarida The Punch ta ce wannan ƙudiri ya biyo bayan zaman majalisar da aka yi a Ibadan, a ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026, inda 'yan majalisar suka jaddada goyon bayansu ga shugabancin ɓangaren zartarwa da na majalisa.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Me majalisa ta ce kan tsige Gwamna Makinde?

Yayin da yake gabatar da ƙudirin, shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanjo Adedoyin, ya bayyana jita-jitar a matsayin mara tushe kuma mai nasaba da siyasa.

A cikin bayaninsa, ya siffanta zarge-zargen da cewa marasa tushe, masu raba hankali, kuma masu nasaba da siyasa, jaridar Tribune ta kawo labarin.

"Majalisar tana nan cikin haɗin kai kuma tana jajircewa wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata, sannan babu wata magana a hukumance ko wani tsari da ke nuna shirin tsigewa da aka fara a cikin majalisar.”

- Sanjo Adedoyin

An musanta batun tsige Olubadan

'Yan majalisar sun kuma lura da rade-radin siyasa na baya-bayan nan, ciki har da iƙirarin da ke alaƙanta Makinde, Olubadan na ƙasar Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, da wasu 'yan majalisa da zargin ƙulla makirci da juna, inda suka bayyana su a matsayin marasa tushe.

A baya dai an samu zarge-zarge a bainar jama'a daga tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, yana nuna cewa ana yin wasu dabarun siyasa da don tsige sarkin, iƙirarin da gwamnatin jihar da fadar sarkin suka musanta.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: ICIR ta fallasa 'boyayyun dalilan' Tinubu na tsige ministoci 2

A zaman na ranar Laraba, mataimakin shugaban majalisar Mohammed Fadeyi ya goyi bayan ƙudirin, inda ya bayyana majalisar a matsayin mai haɗin kai tare da yaba wa gwamnatin Makinde kan ayyukanta a fannonin samar da ababen more rayuwa, ilimi, da kuma kiwon lafiya.

An musanta batun tsige Gwamna Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

An ja kunnen masu yada jita-jita

Babban mai tsawatarwa na majalisar, Gbenga Oyekola, shi ma ya nesanta kansa da iƙirarin tattaunawa kan batun tsigewa, tare da gargaɗin waɗanda ke bayan jita-jitar da su daina.

“Babu rarrabuwar kawuna a wannan majalisa. Mun mayar da hankali ne kan shugabanci da samar da alfanun dimokuraɗiyya ga al'ummar Jihar Oyo ta hanyar wakilci na gari."

- Gbenga Oyekola

Ya ƙara da cewa majalisar ba za ta bari wani mutum ko wata ƙungiya ta yi mata katsalandan ba, sannan ya jaddada goyon bayan 'yan majalisar ga Makinde da Ogundoyin.

Gwamna Makinde ya saukakawa ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kawo tsarin ba da tallafi ga ma'aikata wanda za a rika badawa duk wata.

Gwamnati ta sanar da cewa za a rika bayar da wannan tallafi na N10,000 na tsawon watanni uku domin rage wa ma'aikata radadi.

Gwamna Makinde ya ce an samar da tallafin domin rage radadin da ma’aikata ke fuskanta wajen biyan kudin zirga-zirga saboda tsadar fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng