Martanin da Matawalle Ya Yi kan Zarginsa da ’Yar Majalisar Amurka Ta Yi
- Karamin ministan tsaron ƙasa, Bello Matawalle, ya yi martani kan zargin da wata yar majalisa a Amurka ta yi masa
- Matawalle ya karyata zargin yunƙurin ba da cin hanci ga jami’in Amurka, yana mai cewa labarin ƙarya ne mara tushe
- Ofishinsa ya bayyana cewa rahotannin sun samo asali daga wasu wallafe-wallafen yanar gizo da suka danganta zargin da wani ɗan majalisar Florida
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ofishin karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle ya nuna damuwa game da zargin da ake yi wa tsohon gwamnan.
Ofishin ya ƙaryata zarge-zargen da ke yawo cewa ya yi yunƙurin bai wa wani jami’in Amurka cin hanci.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya bayyana a shafinsa na X a yau Laraba 22 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu
Matawalle ya yi martani ga yar majalisar Amurka
Sanarwar ta ce ta lura da rahotannin da ke yawo wanda ake zargin ministan wanda ya saɓa doka tare da tabbatar da cewa irin wannan labari zai kawo rigima a cikin ƙasa.
Ta bayyana cewa an danganta zargin da wani ɗan majalisar Florida, amma ta jaddada cewa zargin ba shi da tushe ko sahihanci.
Sanarwar ta ƙara da cewa Bello Matawalle bai taɓa shiga harkar cin hanci ba, kuma ba zai taɓa amincewa da duk wani aiki na rashin gaskiya ba.
Ofishin ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe, masu yaudara da kuma wata manufa ta ɓata suna domin karkatar da hankali daga aikinsa.

Source: Twitter
Abin da Matawalle ya mayar da hankali kansa
Sanarwar ta ƙara da cewa ministan yana mai da hankali kan ayyukansa a ma’aikatar tsaro kuma ba zai bari farfaganda ta hana shi ba.
Sanarwar ta ce:
“Ministan yana tsaye daram kuma ba zai bari wannan ya girgiza shi ba, ba kuma zai bari kamfen na ɓata suna ya karkatar da hankalinsa ba.
"A maimakon haka, yana ci gaba da mai da hankali kan nauyin da ke kansa, yana gudanar da ayyukansa da ƙwazo, gaskiya, da kuma jajircewa wajen yi wa ƙasa hidima.
" Saboda haka, ana shawartar jama'a da su yi watsi da waɗannan rahotanni masu yaudara da kuma zarge-zargen da ba su da tushe."
Ofishin ya bukaci jama’a su yi watsi da zargin, yana mai jaddada cewa Matawalle na da ƙwazo, gaskiya da jajircewa wajen yi wa ƙasa hidima.
An roki Tinubu ya sallami Matawalle daga mukaminsa
A wani labarin, an ji cewa yar majalisar jihar Florida, Kimberly Daniels, ta tsoma baki a cikin al'amarin tsaron Najeriya tare da ba Bola Tinubu shawara.
Wani rahoton tsaro da ta gabatar ya nuna karuwar hare-hare a lokacin bukukuwan Easter a jihohin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
Daniels ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya duba shugabancin tsaro tare da ɗaukar mataki a kan Bello Matawalle da sallamarsa daga mukaminsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
