Innalillahi: Yan Bindiga Sun Farmaki Manyan Sarakunan Gargajiya 3 Tare da Ajalin 2, Bayanai Sun Fito

Innalillahi: Yan Bindiga Sun Farmaki Manyan Sarakunan Gargajiya 3 Tare da Ajalin 2, Bayanai Sun Fito

  • An shiga tashin hankali bayan ‘yan bindiga sun hallaka manyan sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti
  • Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da sarakan ke dawowa daga wata ganawa ta tsaro a kauyen Irele-Ekiti
  • Sarakunan sun hada da Elesun na Esun-Ekiti, Oba Babatunde Ogunsakin da Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti – ‘Yan bindiga sun hallaka wasu fitattun sarakai guda biyu a karamar hukumar Ikole da ke jihar Ekiti.

Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da sarakan ke dawo daga wata ganawa ta tsaro a kauyen Irele-Ekiti.

'Yan bindiga sun tafka barna bayan hallaka sarakunan gargajiya
Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Sakaunan Gargajiya 3 a Ekiti. Hoto: Biodun Oyebanji.
Asali: Twitter

Wasu sarakunan gargajiya aka hallaka?

Daily Trust ta tattaro cewa wadanda aka kashen sun hada da Elesun na Esun-Ekiti, Oba David Babatunde Ogunsakin da Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olushola.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas ya shaki iskar 'yanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da Alara na Ara-Ekiti, Oba Adebayo Fatoba ya tsira da kyar daga mugun nufin ‘yan bindigan da suka yi kokarin yin ajalinsa shi ma.

Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun so sace dukkan sarakunan ne guda uku a kan hanyar Oke-ako.

Wane martani 'yan sanda ta yi kan kisan

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Sunday Abutu ya ce:

"Zan nemo karin bayani sannan in sanar da ku yadda ake ciki."

Shugaban karamar hukumar Ajoni, Michael Ogungbemi ya tabbatar da faruwar lamarin ga 'yan jaridu, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Ogungbemi ya yi Allah wadai da kisan manyan sarakunan inda ya ce jami'an tsaro sun bazama cikin daji neman maharan.

Wannan na zuwa ne bayan sace wasu jami'an 'yan sanda uku a jihar Delta da 'yan bindiga suka yi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwamushe mutum 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Akwa Ibom

'Yan bindiga sun sace 'yan sanda 3

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa an sace wasu jami'an 'yan sanda a bakin aiki a jihar Delta.

Jami'an 'yan sandan sun gamu da tsautsayi ne bayan wani ya yi karar cewa an yi masa fashi da kwace.

Jami'an sun dauki matakin tura jami'ai guda uku don nema masa hakkinsa lokacin da abin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel