Gwamnatin Tarayya na Karkatar da Kudaden Asusun FAAC? Gaskiya Ta Fito
- Ma'aikatar kuɗi ta ƙasa ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar gwamnati ko ana kashe kudin a ɓoye ba gaskiya ba ne
- Cire kuɗaɗe daga asusun FAAC ba ɓata kuɗi ba ne, face biyan buƙatun doka kamar tsaro, da kuma maido wa jihohi haƙƙoƙinsu, cewar Taiwo Oyedele
- Gwamnatin tarayya ta kuma soki yadda wasu ke amfani da tsofaffin bayanai da watsi da sauye-sauyen da aka samu a farkon 2026 don sukar gwamnati
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Ma’aikatar kuɗi ta tarayya ta yi martani mai zafi game da rahotannin kafofin yaɗa labarai da ke nuna cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar asusun tarayya ko kuma ana kashe kudin a ɓoye.
Ma'aikatar ta bayyana cewa waɗannan rahotanni sun yi mummunar fassara ga rahoton Bankin Duniya na baya-bayan nan game da ci gaban da Najeriya ta samu.

Source: Twitter
Gwamnati ta na karkatar da kudaden FAAC?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙaramin ministan kuɗi na ƙasa, Taiwo Oyedele, ya sanya wa hannu, kuma ya wallafa a shafinsa na X.
A cikin sanarwar, gwamnati ta bayyana cewa fassarar da aka yi wa rahoton Bankin Duniya ta nuna rashin fahimta game da tsarin kasafin kuɗi na ƙasa.
Gwamnati ta jaddada cewa babu kudin da ya ɓata, kuma an cire kowane kudi daga asusun tarayya bisa tanadin doka, ba tare da karya kowace ka'ida ba.
Sanarwar ta bayyana cewa cire kuɗaɗe daga asusun raba kuɗaɗen tarayya (FAAC) ba ya nufin barnatar da dukiya.
Waɗannan kudaden sun haɗa da tanadin doka, asusun tanadi da jari, kashe-kashen tsaro, da kuma maido wa jihohi da ma’aikatu kudaden da suke da haƙƙi a kai.
Tasirin sabuwar dokar da aka zartar
Bugu da ƙari, ma'aikatar ta soki yadda wasu ke amfani da tsofaffin bayanai suna watsi da sauye-sauyen da aka samu a farkon shekarar 2026.
"Sabuwar dokar zartarwa da aka sanya wa hannu a bana tana ƙarfafa yadda ake turo kudaden man fetur zuwa asusun gwamnati, wanda ake sa ran zai ƙara yawan kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu da kashi 0.4 na GDP a duk shekara."
- Taiwo Oyedele.
Ma'aikatar ta jawo hankali kan cewa ainihin saƙon Bankin Duniya yana nuna ci gaba ne, ba nakasu ga Najeriya ba.

Source: Instagram
Ci gaban da aka samu a Najeriya
A cewar ministan:
"Rahoton ya nuna cewa tattalin arziƙin Najeriya yana haɓaka a sassa daban-daban, hauhawar farashin kaya na raguwa sakamakon manufofin gwamnati, sannan asusun ajiyar ƙasar na waje ya ƙarfafa.
"Haka kuma, an sami raguwar nauyin bashi idan aka kwatanta da girman tattalin arziƙin ƙasa a karon farko cikin shekaru goma."
A ƙarshe, gwamnatin tarayya ta sake jaddada aniyarta na samar da gaskiya da riƙon amana a fannin sarrafa kuɗaɗen jama'a.
Tinubu ya nada Taiwo Oyedele minista
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon minista a Najeriya domin kara inganta ayyukan gwamnatinsa.
Shugaban ya Taiwo Oyedele a matsayin Karamin ministan kudi domin maye gurbin Dr. Doris Uzoka-Anite da aka sauyawa ma'aikata.
Hakan ya biyo bayan shirin maye gurbin Uzoka-Anite, wacce za ta koma Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare ta Kasa a matsayin karamar minista.
Asali: Legit.ng

