Tinubu Ya Nada Sababbin Ministoci 2 da Ya Fatattaki Wale Edun da Ahmed Dangiwa
- Shugaba Bola Tinubu ya yi garambawul a majalisar zartarwa ta tarayya ta hanyar sallamar ministoci biyu, Wale Edun, da Ahmad Dangiwa
- Taiwo Oyedele ne zai karɓi ragamar ma'aikatar kuɗi, yayin da aka naɗa Muttaqha Rabe Darma (PhD) domin ya jagoranci ma'aikatar gidaje da birane
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya bayyana manyan dalilan da suka sanya Tinubu ya yi sauye sauye a majalisar ministocinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, ya yi ƙarin haske game da dalilan da suka sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul a majalisar zartarwa ta ƙasa.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya sallami Wale Edun daga mukamin ministan kudi yayin da aka sallami Ahmed Dangiwa daga mukamin ministan gidaje.

Source: Twitter
Dalilin Bola Tinubu na tsige ministoci
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 21 ga Afrilu, 2026, Akume ya bayyana cewa sauye-sauyen sun zama dole domin ƙarfafa haɗin kai da kuma samar da jituwa a tafiyar da gwamnati, in ji rahoton Daily Trust.
Ya jaddada cewa babban burin shugaban ƙasar shi ne ganin an samu ci gaba mai ma'ana a fannin tattalin arziƙi wanda ƴan Najeriya za su ji a jikinsu, daidai da manufofin "Renewed Hope Agenda."
Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi amfani da cikakken ikon da doka ta ba shi wajen gudanar da wannan garambawul.
Ya yi nuni da sassan 147 da 148 na Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tasrayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi masa gyara), waɗanda suka ba shugaban ƙasa ikon naɗawa ko sallamar mambobin majalisar ministocinsa a duk lokacin da ya ga hakan ya dace.
Sababbin ministocin da Tinubu ya nada

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Sanata George Akume ya sanar da sunayen sababbin ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada domin maye gurbin wadanda aka sallama, in ji rahoton Punch.
Tinubu ya amince da nadin Taiwo Oyedele, wanda kafin yanzu shi ne Karamin Ministan Kudi, domin ya zama Ministan Kudi kuma babban minista mai kula da tattalin arzikin kasa.
Haka zalika, Tinubu ya nada Muttaqa Rabe Darma (PhD) a matsayin wanda zai shugabanci Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane.
An umarci tsohon ministan ma'aikatar, Ahmed Dangiwa, da ya mika ragamar ma'aikatar ga Karamin Ministan da ke karkashinsa yayin da ake jiran kammala tantance Muttaqha Darma.

Source: Twitter
Wa'adin mika ragamar shugabanci
Sanarwar ta bayyana cewa dole ne a kammala dukkan tsare-tsaren mika ragamar aiki da karbar sabon matsayi a kowane mataki kafin a tashi daga aiki a ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026.
Wannan na nufin gwamnati tana son ganin sababbin ministocin sun fara aiki cikin gaggawa domin kauce wa duk wani tsaiko a harkokin mulki, musamman a fannin tattalin arziki.
Shugaba Tinubu ya mika godiyarsa ga tsofafin ministocin biyu, Wale Edun da Umar Dangiwa, saboda hidimar da suka yi wa kasa, inda ya yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba.
Alkawarin minista na samar da gidaje
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na samar da gidaje masu saukin farashi domin tallafawa ‘yan kasa masu karamin karfi.
Ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa ana shirin gabatar da wani sabon tsarin kudi domin jama’a su mallaki gida cikin sauki.
Ahmed Dangiwa ya kara da cewa ce gwamnati za ta kafa cibiyoyin kera kayan gini a yankuna shida na kasar domin rage dogaro da kasashen ketare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

