Malami Ya Umarci Mabiyansa a Najeriya Su ba Yan Bindiga Lambar Wayarsa idan Aka Sace Su

Malami Ya Umarci Mabiyansa a Najeriya Su ba Yan Bindiga Lambar Wayarsa idan Aka Sace Su

  • Fitaccen limamin coci a Najeriya, Bishof David Oyedepo ya ce mabiyansa na da wani karfin iko da Ubangiji ya ba su don magance matsaloli
  • Oyedepo ya bukaci duk wani mabiyinsa da 'yan bindiga suka sace ya ba su lambarsa, yana mai cewa yana da lakanin kubutar da mutane
  • Ya bayar da misalin wani fasto da aka sace, inda masu garkuwar suka ba shi damar yin magana da shi ta waya kuma ya cece shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - Jagoran cocin Living Faith Church Worldwide da ke jihar Ogun, Bishof David Oyedepo, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya umarci mabiyansa su ba 'yan bindiga lambarsa idan aka sace su.

Fitaccen malamim addinin kiristan ya yi ikirarin cewa yanada lakani daga Ubangiji da zai iya kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane cikin sauki.

Kara karanta wannan

Ningi: Babban kuskuren da zai hana wasu sanatoci da 'yan majalisu koma wa kujerunsu a 2027

David Oyedepo.
Babban limamin coci a Najeriya, Bishof David Oyedepo yana tsakiyar wa'azi a jihar Ogun Hoto: Bashop David Oyedepo
Source: Twitter

Limamin coci ya cika baki kan masu garkuwa

Oyedepo ya bayyana hakan ne yayin wani wa’azi a Canaanland, inda ya bukaci mabiya cocin kada su firgita idan aka sace su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

“Idan wani ya sace ka, ka ba shi lambata,” in ji shi a cikin hudubar da ya yi, wacce daga baya ta yaɗu a kafafen sada zumunta.

Malamin ya danganta wannan kira da wasu abubuwan da ya ce sun faru a baya, inda aka sace wasu mabiya cocin kuma ya kubutar da su.

Yadda Oyedebo ya kubutar da wasu

Ya bayar da misalin wani fasto da yan bindiga suka sace, inda masu garkuwar suka ba shi damar yin magana da shi ta waya.

A cewarsa, ya gargadi masu garkuwar cewa su sake mutumin cikin sa’o’i 24 ko kuma su fuskanci mutuwa, lamarin da ya ce daga bisani ya kai ga sakin wanda aka sace.

Kara karanta wannan

Bayan boye boye saboda yaƙin Iran, Netanyahu ya fadi halin lafiyarsa

Haka kuma, ya ambaci wata mace da aka sace wadda ta yi wa kanta addu'ar cewa za a sake ta kafin ƙarfe 7:00 na safe, kuma daga baya aka sake ta.

Oyedepo.
Babban limamin coci a jihar Ogun, Bishop David Oyedepo yana jawabi a zaman cocinsa Hoto: Bishop David Oyedepo
Source: Facebook

Malamin ya fadi karfin mabiyansa

Oyedepo ya ce waɗannan abubuwa suna nuna cewa mabiyansa suna da karfin iko da Ubangiji ya ba su, wanda ya fi ƙarfin duk wani abin tsoro ko tashin hankali.

“An ɗaukaka ku sama da shaidan,” in ji shi, yana mai ƙarfafa musu gwiwa su fuskanci barazana da imani maimakon su ji tsoro.

Ya kuma ƙara da cewa duk mabiya cocin suna da wannan karfi na Ubangiji, don haka ya kamata su koyi yadda za su yi amfani da shi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Oyedepo ya hango makomar 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen limamin coci, Bishof David Oyedepo ya ce nan da yan kwanaki 'yan bindiga da masu daukar nauyinsu za su gamu da hukuncin Ubangiji.

Malamin ya kara da cewa ramuwar Ubangiji za ta tabbata kan wadannan masu laifi cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa hakan ba zai dauki lokaci mai tsawo ba.

Oyedepo ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa nan gaba kadan ‘yan Najeriya za su fara ganin sakamakon abin da ya kira daukin Allah cikin lamarin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262