Arewa da Kudu Za Su Amfana da Tinubu Ya Nemi Izinin Sake Ciyo Bashin Dala Miliyan 516

Arewa da Kudu Za Su Amfana da Tinubu Ya Nemi Izinin Sake Ciyo Bashin Dala Miliyan 516

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya aika wasikar neman izinin karbo aron kudi daga bankin Jamus zuwa Majalisar Dattawan Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya shaida wa sanatoci cewa yana son karbo rancen Dala miliyan 516.3 domin gina titin Sokoto zuwa Badagry
  • Ana sa ran titin zai bunƙasa kasuwanci, samar da abinci, da haɗa yankunan noma da kasuwanni da tashoshin jiragen ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi izinin Majalisar Dattawa domin sake ciyo bashin Dala miliyan 516.3 daga bankin Deutschk da ke kasar Jamus.

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kinkimo wannan rancen ne domin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya halarci zaman Majalisar tarayya don gabatar da kasafin kudi Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A wata wasiƙa da aka karanta a zauren majalisar, shugaban ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 1,000 zai haɗa Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Amurka za ta jefa Iran a sabuwar matsala, fada ya koma kan gasar cin kofin duniya

Bayanin aikin da Tinubu zai yi da kudin

A cewar shugaban kasar, hanyar za ta tashi daga Illela a jihar Sokoto ta ratsa ta jihohin Kebbi, Neja, Kwara, Oyo da Ogun kafin ta ƙare a Badagry da ke jihar Legas.

Tinubu ya bayyana cewa za a samu aron kudin ne ta hanyar haɗin gwiwar bankuna ƙarƙashin jagorancin Deutsche Bank AG, tare da kariya daga Islamic Corporation for the Insurance of Investment and Export Credit (ICIEC)

Ya ce gwamnatin tarayya kuma za ta bayar da gudummawar Naira biliyan 265.5 domin biyan diyya, mallakar ƙasa da sauran ayyuka masu alaƙa da gina titin.

Yadda Najeriya za ta biya bashin

A cewar wasiƙar, za a yi amfani da bashin wajen gina sashe na 1, rukuni na 1a da 1b, mai nisan kilomita 120, cikin baki daya kilomita 1,000.

Aron wadannan kudi zai ɗauki shekaru tara kafin a biya, ciki har da jinkirin fara biyan bashin na shekaru uku, tare da ribar da ba za ta wuce ƙa’idar SOFR na CME da ƙarin kashi 5.3 cikin ɗari ba.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Amfanin titin Sokoto zuwa Badagry

Shugaban ƙasa Tinubu ya ce wannan hanya za ta inganta haɗin kai tsakanin Arewa da Kudu, ta ƙara tsaro, tare da rage kuɗin sufuri, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

"Haka kuma, ana sa ran za ta bunƙasa kasuwanci, samar da abinci, da haɗa yankunan noma da kasuwanni da tashoshin jiragen ruwa," in ji shi.
Majalisar Dattawa.
Zauren Majalisar dattawa yayin da sanatocinke taakiyar zama a Abuja Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya miƙa buƙatar ga kwamitin kula da basussuka na cikin gida da na waje domin nazari, kuma ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahoto cikin mako guda.

Ana bin kowane dan Najeriya bashin N724,000

An ji cewa alkaluma daga Hukumar Kula da Harkokin Bashi ta Kasa (DMO) sun nuna cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa karshen 2025.

Hakan na nufin idan aka raba wadannan kudade kan 'yan Najeriya, kowane mutum daya ana bin shi bashin kusan N724,000, a cewar wani bincike.

Rahoton ya nuna cewa wannan adadi bai haɗa da sabon bashin Naira tiriliyan 8.3 da aka amince Tinubu ya ciyo ba a 226, wanda hakan na nufin adadin zai iya karuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262