An Fara Tantance Muttaqha Darma a Majalisar Dattawa bayan Tinubu Ya Nada Shi Minista
- Sabon ministan da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada, Dr. Muttaqa Rabe Darma ya gurfana a gaban Majalisar dattawa don tantance shi
- Rahotanni sun nuna cewa sanatoci sun titsiye shi da tambayoyi a zamansu na yau Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026
- Ana sa ran Majalisar za ta tabbatar da nadinsa da zaran ta kammala wannan tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta fara tantance Muttaqa Rabe Darma daga jihar Katsina, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin ministan gidaje da raya birane.
Darma ya isa cikin zauren majalisar da misalin ƙarfe 12:32 na ranar yau Alhamis, inda ya bayyana gaban sanatoci domin gudanar da tantancewar da kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan
Darma: Sabon Ministan da Tinubu ya nada ya san matsayarsa bayan tantance shi a majalisa

Source: Facebook
Majalisar dattawa ta fara tantance Darma
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tuni sanatoci suka fara yi masa tambayoyi kan ƙwarewarsa, manufofinsa da kuma shirinsa na jagorantar ma’aikatar gidaje.
Wannan mataki ya biyo bayan wasiƙar da shugaban ƙasa ya aika wa majalisar a ranar Laraba, yana neman amincewa da naɗin Darma a matsayin minista.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar, kafin ya miƙa ta ga kwamitin duka majalisa domin nazari, tare da umarnin su gabatar da rahoto cikin gaggawa.
Takaitaccen bayani kan sabon minista
Dr. Muttaqa Rabe Darma ƙwararren injiniya ne, wanda ya kammala karatun Mechanical Engineering a Jami’ar Bayero da ke jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ana sa ran zai kawo ƙwarewa ta fasaha a ma’aikatar gidaje, wadda ke da muhimmanci wajen magance ƙarancin gidaje da matsalolin gine-ginen birane a Najeriya.
A zaɓen 2023, Darma ya kasance mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, amma daga bisani aka kore shi bayan ya goyi bayan ɗan takarar APC, Malam Dikko Radda.

Kara karanta wannan
Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516
Sanatoci sun titsiye shi a Majalisa
Duk da wannan, wasu na ganin naɗin nasa ya dace da ƙoƙarin gwamnati na amfani da ƙwararru wajen tafiyar da ma’aikatu, musamman a ɓangaren gidaje.

Source: Facebook
A yayin zaman majalisar dattawa yau Alhamis, sanatoci sun yi wa Darma tambayoyi masu zurfi kan yadda zai magance matsalar ƙarancin gidaje da ke addabar ƙasar nan, idan aka ba shi ma’aikatar gidaje.
Muttaqa Darma ya gabatar da ra’ayoyinsa da tsare-tsarensa kan yadda za a inganta ɓangaren gidaje da rage gibi da ake fama da shi, kuma na sa ran Majalisa za ta yanke hukunci nan kusa.
Ministan Tinubu ya yi murabus
A wani rahoton, kun ji cewa Adebayo Adelabu ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin makamashi domin neman takarar gwamna a jihar Oyo.
Hakan na kunshe ne a cikin wasikar murabus dinsa mai dauke da ranar 22 ga Afrilu, 2026, wacce ya mika wa Shugaba Tinubu ta hannun sakataren gwamnatin tarayya.
Rahotanni sun nuna cewa ministan ya sanar da shirinsa na yin murabus bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng