Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Kai Sababbin Hare Hare a Plateau Aka Rasa Rayuka
- An sake shiga jimami a jihar Plateau bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci
- Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki wasu kauyuka guda biyu inda suka hallaka bayin Allah tare da raunata wasu daban
- An koka da cewa an sanar da jami'an tsaro bullar wasu bakin mutane da ba a yarda da su amma ba a dauki mataki ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Mazauna wasu kauyuka biyu a jihar Plateau sun sake afkawa cikin yanayin jimami biyo bayan wasu hare-haren 'yan bindiga.
Hare-haren na 'yan bindiga sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane shida, yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti.

Source: Facebook
Yayin da yake magana da tashar Channels Tv ta wayar tarho, sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, Tengong Rwang, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga da masu daukar nauyinsu sun shiga uku, an ji abin da zai faru da su a Najeriya
'Yan bindiga sun yi barna a Plateau
Lamarin, wanda ya faru a kauyen Shonun da ke karamar hukumar Riyom da kuma Hurum da ke gundumar Gashish a karamar hukumar Barkin Ladi, ya sake rura wutar damuwa kan matsalar rashin tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin.
Tengong Rwang ya bayyana cewa hare-haren sun faru ne daban-daban a dare guda, inda aka bayar da rahoton cewa maharan sun zo ne a ƙasa kuma suna ɗauke da mugayen makamai.
A cewarsa, an kashe mutane huɗu a Hurum, yayin da wasu biyar suka ji raunuka kuma a halin yanzu suna karɓar magani.
A Shonun kuma, ya ce an tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu uku ke asibiti sakamakon hare-haren, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
An sanar da jami'an tsaro
Rwang ya yi zargin cewa kafin faruwar lamarin, mazauna Shonun sun tada jijiyar wuya game da kwararar wasu makiyaya da ba a san su ba zuwa yankin, lamarin da ya ce an kai rahotonsa ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai farmaki fada, sun yi garkuwa da mai martaba Sarki a Najeriya
“Mutanen Shonun sun riga sun sanar da jami’an tsaro game da motsin mutanen da ba a yarda da su ba a cikin kauyen amma kamar ba a yi komai ba."
- Tengong Rwang
Yayin da yake bayyana kauyukan da abin ya shafa a matsayin waɗanda suka daɗe suna shan wahala, Rwang ya lura cewa maimaita hare-hare tsawon shekaru ya sa mazauna da dama sun rasa matsugunansu, inda wasu da dama suka gudu zuwa garuruwa mafi tsaro.

Source: Original
“Waɗannan kauyuka ne da suka sha fama da hare-hare akai-akai. Yawancin mutane sun bar gidajensu saboda tsoron kada a kashe su."
- Tengong Rwang
Ya bayyana cewa 'yan sa-kai sun yi ƙoƙarin fatattakar maharan amma ƙarfinsu ya gaza saboda maharan suna da manyan makamai, wanda hakan ya yi sanadiyyar mace-macen da aka samu.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Lokacin da aka tuntubi jami’in yaɗa labarai na rundunar ’yan sandan jihar Plateau, Alfred Alabo, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani a hukumance kan lamarin ba.
Sai dai ya ba da tabbacin cewa za a bayar da ƙarin bayani bayan an samu bayanai daga manyan jami’an ’yan sanda (DPOs) na yankunan da abin ya shafa.

Kara karanta wannan
Sojoji sun samu nasarar cafke mataimakin fitaccen jagoran 'yan bindiga da matarsa
'Yan bindiga sun kashe basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wani basarake a jihar Imo da ke yankin Arewa maso Gabas.
Yan bindigan sun kashe basaraken na mazaɓar Ochia Awarra Ohaji, Ochia Paulinus Ekwueme, har lahira a kan iyakar kauyukan Assa da Ochia.
An yi wa basaraken da jami’an tsaron da ke tare da shi kwanton-bauna ne a kan iyakar kauyukan Assa da Ochia.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng