Yadda Yaƙin Iran da Isra'ila Zai Jefa Masu Amfani da Kororon Roba a Matsala
- Farashin kwaroron roba na duniya na iya tashi sosai bayan rikicin Iran ya haddasa tangarda a hanyoyin samar da kayayyaki
- Kamfanin Karex ya bayyana cewa zai kara farashi da kaso 20 zuwa 30 saboda karin kudin jigila da jinkirin kaya da ke haddasa karancin kaya
- Masana sun gargadi cewa ci gaba da wannan matsala zai iya jawo karanci musamman a kasashe masu karamin karfi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Kamfanin Karex da ke samar da kororon roba ya bayyana cewa zai kara farashi da kaso 20 zuwa 30.
Kamfanin ya ce hakan na da nasaba da karin kudin jigila da jinkirin kaya da ke haddasa karancin samar da shi.

Source: Facebook
Ana fargabar tashin farashin kororon roba
Rahoton TheCable ya ce farashin zai iya karuwa sosai sakamakon tangardar hanyoyin samar da kayayyaki da rikicin Iran ya janyo.
Kamfanin Karex, mafi girma wajen samar da kwaroron roba a duniya, ya ce yana shirin kara farashi tsakanin kaso 20 zuwa 30, tare da yiwuwar karin idan matsalar ta ci gaba.
Babban jami’in kamfanin, Goh Miah Kiat, ya bayyana cewa hauhawar kudin jigila da jinkirin kaya sun rage yawan kayayyaki.
Ya ce:
“Yanayin na da matukar rauni, domin kudade na karuwa a fannoni daban-daban, kuma babu zabi face a dora wasu daga cikin karin kudin ga abokan hulda”.

Source: Getty Images
Yawan kororon roba da Karex ke samarwa
Karex na samar da fiye da kororon roba biliyan biyar a duk shekara, kuma yana samar wa manyan kamfanoni da shirye-shiryen kiwon lafiya na duniya kayayyaki.
Rikicin Gabas ta Tsakiya ya janyo matsaloli wajen samar da makamashi da sinadarai, wanda hakan ya shafi samun kayan aiki masu muhimmanci wajen samar da kayayyaki.
Goh ya kara da cewa tun bayan tsanantar rikicin, kudin samar da kayan kamar roba na sinadarai, nitrile da kayan marufi sun karu sosai.
Duk da cewa kamfanin na da isassun kaya na dan lokaci, yana kara yawan samarwa domin biyan bukatar da ta karu da kusan kaso 30 a bana.
Lokutan jigilar kaya ma sun tsawaita, inda yanzu ake daukar kusan watanni biyu kafin kayayyaki su isa Turai da Amurka, sabanin wata guda a baya.
Ya ce ana samun jinkiri sosai a jigilar kaya a teku, duk da cewa bukata na karuwa, kuma kasashe masu tasowa na fuskantar karanci, cewar Leadership.
An kuma danganta matsalar da raguwar ajiyar kayayyaki a duniya sakamakon rage tallafin kasashen waje, musamman daga hukumar USAID.
Iran za ta kai harin ramuwar gayya
An ji cewa kasar Iran ta ce ba ta da niyyar halartar tattaunawa da Amurka domin gano ko za a iya kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.
An shirya tattaunawar zagaye na biyu tsakanin Amurka da Iran a Pakistan bayan zagaye na farko da mataimakin shugaban Amurka ya halarta.
Sai dai Iran ta zargi Amurka da toshe tashoshin jiragen ruwa tare da kai farmaki kan jirgin ruwanta, lamarin da ya kara dagula lissafi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

