Iran Ta Jingine Batun Zaman Sulhu bayan Amurka Ta Kai wa Jirginta Hari, Ta Shirya Ramuwa
- Iran ta ce ba ta da niyyar halartar tattaunawa da Amurka domin gano ko za a iya kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya
- An shirya tattaunawar zagaye na biyu tsakanin Amurka da Iran a Pakistan bayan zagaye na farko da mataimakin shugaban Amurka ya halarta
- Sai dai Iran ta zargi Amurka da toshe tashoshin jiragen ruwa tare da kai farmaki kan jirgin ruwanta, lamarin da ya kara dagula lissafi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Iran – Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ce ba ta da shirin halartar sabuwar tattaunawa da Amurka a ƙasar Pakistan, duk da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump.
Tuni Amurka ta sanar da cewa ta aikata tawagarta da ake sa ran za ta sauka a Pakistan a yau Litinin, 20 ga watan Afrilu na shekarar 2026 domin ci gaba da tattaunawa.

Source: Twitter
Middle East eye ta wallafa cewa matakin na zuwa ne yayin da ake dab da zuwa ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta da ta dakatar da rikicin da ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya da aka cimma da farko.
Ana samun tsaiko kan hana wa da Iran
The Times of India ta ruwaito cewa rikicin ya samo asali ne bayan hare-haren ba-zata da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Babban abin da ke kawo tsaiko a tattaunawar shi ne toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran da Amurka ke yi, wanda Tehran ke ganin dole ne a dage kafin a ci gaba da zaman sulhu.
Rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu babu wani shiri na shiga zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a Pakistan.
Iran ta nuna cewa buƙatun Amurka ba su da ma’ana, lamarin da ke rage yiwuwar samun maslaha mai dore wa a yaƙin da ya fara salwantar da rayukan bayin Allah da dama.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Kasar Musulunci ta Iran ta jikawa Amurka aiki ana shirin komawa teburin sulhu
Ana kara samun barazana a yaƙin Iran
Sababbin rikice-rikice sun sake kunno kai bayan wani jirgin ruwan yakin Amurka ya harba tare da kwace wani jirgin Iran da ya yi ƙoƙarin tsallake katangar ruwa da Amurka ta kafa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa jirgin ruwan Iran mai suna Touska ya yi yunƙurin kauce wa katangar, amma sojojin ruwan Amurka sun tilasta masa tsayawa bayan lalata injinsa.

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa a yanzu sojojin Amurka sun karɓi iko da jirgin. A martanin da ta mayar, Iran ta ce za ta ɗauki fansa, inda aka rawaito cewa ta aika jiragen sama marasa matuƙa domin bin jiragen ruwan Amurka.
Wannan sabon rikici ya ƙara tsananta halin da ake ciki musamman a mashigar ruwa ta Hormuz, da ke da muhimmanci wajen jigilar kusan kas1/5% na man fetur da iskar gas na duniya.
Iran ta sabunta makamai
A baya, kun samu labarin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara gyara makamanta da sabunta wasu daga cikinsu a yayin tsagaita wuta da ake yi da Amurka.

Kara karanta wannan
Lissafi ya canza, Iran ta tura sako 'mara dadi' zuwa Amurka kan batun zaman sulhu
An gyara na’urorin harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da suka samu matsala a yayin yakin Amurka da Isra'ila suka fara a watan Fabarairu, 2026.
Rikici ya sake ɗaukar zafi bayan batun rufe mashigar Hormuz da barazanar Amurka yayin da ake hasashen zaman sulhu ko zai yiwu bayan harin jirgin ruwan Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
