Miji na zargin matar sa da cin amana saboda ya ga kororon roba a jakar ta

Miji na zargin matar sa da cin amana saboda ya ga kororon roba a jakar ta

- Wata mace ta shigar da mijinta kara kotu inda take bukatar a raba aurensu saboda ya cika fitina

- Tayi ikirarin cewa fitinar mijinta ne ya janyo ta kamu da ciwon hawan jini

- Mijin ya nuna wa kotu kororon roba wanda ya gano cikin jakar matarsa a matsayin hujjar tana zina

Cikin hawaye, wani magidanci mai yara uku, Oluyomi Ogunsanya, ya gabatarwa wata kotu da ke zamanta a Mapo, Ibadan, kwalin kwaroron roba na mata a matsayin hujja da ke nuna cewa matarsa mai suna Sherifat tana bin wasu mazaje a waje.

Sai dai Sherifat wadda ma'aikaciya ce a Jami'ar Olabisi Onabanjo da ke Ago-Iwoye na jihar Ogun ta roki kotu ta raba aurensu. Ta kuma shaidawa kotu cewa kororon roban da Ogunsanya ya gabatarwa kotu kyauta ce da ma'aikatan lafiya suka bata.

Miji ya gabatar da kwandom a gaban kotu a matsayin shaidar matarsa na aikata zina
Miji ya gabatar da kwandom a gaban kotu a matsayin shaidar matarsa na aikata zina
Asali: Twitter

Matar ta ce fitinar mijinta ya ishe ta har ta kamu da ciwon hawan jini saboda hakan ta ke rokon kotu ta raba aurensu.

DUBA WANNAN: Wani gwani a Kudu ya tsine wa duk mai sauya jam'iyya zuwa APC

Ta ce, "Kullum kokarinsa shine tayar da fitina a gida hakan yasa na kamu da hawan jini. Baya kulawa da yaran mu sai dai bala'i kawai. Ina rokon a rabu mana gida. Mun gina gidan mu na farko tare amma ni kadai na gina gidanmu na biyu. Ni dai na gaji dashi."

Idanunsa cike da hawaye, Ogunsanya ya ce yana kulawa da yaransa da matarsa da ke neman a raba su.

Ya kuma shaidawa kotu cewa yana da hujja cewa matarsa na bin mazaje duk da irin kokarin da yake na kulawa da iyalinsa.

Alkalin kotun, Cif Odunade Ademola, ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Oktoba. Ya ce ya bayar da lokaci mai tsawo ne saboda ya bawa manyan yaran ma'auratan damar sasantasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel